Yakin da Isra'ila ke yi da Falasɗinawa da suka yi wa ƙawanya a Gaza - wanda yanzu yake a rana ta 171 - ya kashe mutane aƙalla mutum 32,226 tare da jikkata mutum 74,518. 2300 GMT — An hana hukumar kula da Falasɗinawa ta MDD kai kayan agaji arewacin Gaza Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da ƴan gudun hijirar Falasɗinu ta bayyana cewa haƙiƙa Isra’ila ta hana ta kai kayan agaji a arewacin Gaza, inda ake fuskantar barazanar yunwa. "Duk da wannan bala'i da ke faruwa a kan idanuwanmu, hukumomin Isra'ila sun sanar da Majalisar Ɗinkin Duniya cewa ba za su sake amincewa da wani ayarin abinci na hukumar @UNRWA zuwa arewa ba," in ji Shugaban hukumar, Philippe Lazzarini a wani saƙo da ya wallafa a shafin X. "Wannan abin ban tsoro ne kuma ana yi ne da gayya don hana taimakon ceton rai a daidai lokacin da ake fama da tsananin yunwa wacce aka sabbaba ta da gangan." Daraktar sadarwa ta UNRWA Juliette Touma ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an yanke shawarar ne a wata ganawa da ta yi da jami'an sojin Isra'ila. Hakan ya biyo bayan hana jigilar ayarin motocin zuwa arewa a makon da ya gabata, inda aka aika musu batun hanin a rubuce. Ba a bayar da dalilin ɗaukar matakin ba, in ji Touma. Gaza na fuskantar mummunan yanayi na jinƙai sakamakon mummunan yakin da Isra'ila ke yi a yankin, wanda aka fara kusan watanni shida da suka gabata bayan farmakin ba-zata da Hamas ta kai a Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba. 1924 GMT — Jami'in Hamas ya ce an samu bambanci mai tsanani da Isra'ila a tattaunawar Gaza Akwai bambance-bambance masu zurfi tsakanin Hamas da Isra'ila a tattaunawar sulhun Gaza, kamar yadda wani jami'in kungiyar gwagwarmayar Falasdinu da ke da masaniya kan tattaunawar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP. Jami'in ya ce "Akwai banbanci mai zurfi a cikin shawarwarin da ake yi tsakanin Hamas da Isra'ila ƴan mamaya, saboda maƙiya sun ɗauki sassaucin da ƙungiyar Hamas ke nunawa a matsayin rauni."
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Kai-tsaye: An hana hukumar kula da Falasɗinawa ta MDD kai kayan agaji arewacin Gaza
Yakin da Isra'ila ke yi da Falasɗinawa da suka yi wa ƙawanya a Gaza - wanda yanzu yake a rana ta 171 - ya kashe mutane aƙalla mutum 32,226 tare da jikkata mutum 74,518. 2300 GMT — An hana hukumar kula da Falasɗinawa ta MDD kai kayan agaji arewacin Gaza Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da...

Yakin da Isra'ila ke yi da Falasɗinawa da suka yi wa ƙawanya a Gaza - wanda yanzu yake a rana ta 171 - ya kashe mutane aƙalla mutum 32,226 tare da jikkata mutum 74,518. 2300 GMT — An hana hukumar kula da Falasɗinawa ta MDD kai kayan agaji arewacin Gaza Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da...
