Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Kai-tsaye: An gina 'ramin tsaro' a babban birnin Iran bayan harin da Isra'ila ta kai

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 403 — ya kashe akalla Falasdinawa 43,603 da jikkata 102,929, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,243 tun Oktoban bara. Talata, 12 ga Nuwamban 2024 0821 GMT — An gina 'ra...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
Kai-tsaye: An gina 'ramin tsaro' a babban birnin Iran bayan harin da Isra'ila ta kai
De un vistazo

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 403 — ya kashe akalla Falasdinawa 43,603 da jikkata 102,929, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,243 tun Oktoban bara. Talata, 12 ga Nuwamban 2024 0821 GMT — An gina 'ra...

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 403 — ya kashe akalla Falasdinawa 43,603 da jikkata 102,929, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,243 tun Oktoban bara. Talata, 12 ga Nuwamban 2024 0821 GMT — An gina 'ramin tsaro' a babban birnin Iran bayan harin da Isra'ila ta kai Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya bayar da rahoton cewa, Iran na gina wasu "ramin tsaro" a Tehran babban birnin kasar, biyo bayan harin da Isra'ila ta kai kan wasu yankuna a kasar. Ramin wanda ke kusa da tsakiyar birnin, zai hada tashar da ke tashar jirgin kasa ta Tehran da asibitin Imam Khumaini, ta yadda za a ba da damar shiga karkashin kasa kai tsaye zuwa asibitin. "A karon farko a kasar, ana gina rami mai dauke da aikace-aikacen kariya a Tehran," in ji shugaban kula da harkokin sufuri na majalisar birnin Tehran ya shaida wa Tasnim . Ƙarin labarai ???? 0923 GMT — Sojojin Isra'ila sun ba da umarnin kwashe mutane daga wasu unguwanni a kudancin Lebanon Sojojin Isra'ila sun umurci mazauna unguwanni uku a kudancin Beirut da su fice daga yankunansu gabanin kai hare-hare ta sama. Sanarwar da sojoji suka fitar ta umurci mazauna yankin da su nisanci mita 500 daga gine-gine da dama a unguwannin Haret Hreik da Ghobeiry da Al-Leik a yankin kudancin Beirut. A cikin sanarwar, an maƙala taswirar gine-ginen da aka yi niyyar kai wa harin, tana mai cewa za a far wa ƙungiyar Hezbollah “da ƙarfi” a kan abin da ta kira kadarori da muradun ƙungiyar a yankin. Sojojin Isra'ila sun sha ba da umarnin kwashe fararen hula a yankuna da dama na kasar Lebanon tun bayan fara kai hare-hare ta sama kan kasar a karshen watan Satumba. 0923 GMT — Kungiyoyin agaji sun ce Isra’ila ta gaza biyan bukatun Amurka na kawo saukin bala’in Gaza Kungiyoyin ba da agaji na ƙasa da ƙasa sun bayyana cewa, Isra'ila ta gaza cim ma jerin buƙatu na Amurka da ke da niyyar inganta ayyukan jin ƙai a Gaza zuwa wa'adin da aka bayar na ranar Talata. Amurka ta shaida wa ƙawayenta Isra'ila a wata wasiƙa a ranar 13 ga watan Oktoba cewa dole ne ta dauki matakin inganta harkokin agaji cikin kwanaki 30. Idan ba haka ba, tana iya fuskantar yuwuwar hani kan taimakon sojojin Amurka. "Ba wai kawai Isra'ila ta gaza cika ƙa'idojin Amurka da za su nuna goyon baya ga ayyukan jin kai ba, amma a lokaci guda ta dauki matakan da suka ƙara dagula lamarin a kasa, musamman a arewacin Gaza," in ji wani rukunin kungiyoyin agaji takwas da suka hada da Oxfam da Save the Children da Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Norway ta ce a cikin rahoton mai shafi 19.