Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

KAI-TSAYE: An dakatar da 'yan sandan Isra'ila biyu kan kai wa dan jaridar Turkiyya hari

Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0930 GMT — Dakarun Isra'ila sun raunata Falasdinawa biyar a Gabar Yamma da Ko...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
KAI-TSAYE: An dakatar da 'yan sandan Isra'ila biyu kan kai wa dan jaridar Turkiyya hari
De un vistazo

Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0930 GMT — Dakarun Isra'ila sun raunata Falasdinawa biyar a Gabar Yamma da Ko...

Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0930 GMT — Dakarun Isra'ila sun raunata Falasdinawa biyar a Gabar Yamma da Kogin Jordan Dakarun Isra’ila sun raunata Falasdinawa biyar, daga ciki har da yaro karami a biranen da ke fadin Gabar Yamma da Kogin Jordan, kamar yadda hukumomin Falasdinu suka tabbatar. Kungiyar bayar da agaji ta Palestinian Red Crescent ta bayyana ma’aikatanta sun shiga lamarin bayan da sojojin Isra’ila suka raunata mutum biyar a Bethlehem da Hebron da Nablus. Ta bayyana cewa akwai Falasdinawa uku da aka harba da bindiga sannan mutum biyu suka samu rauni sakamakon harin. Gabar Yamma da Kogin Jordan na daga cikin wuraren da dakarun na Isra'ila ke kai wa hari. / Hoto: Reuters 0900 GMT — An dakatar da 'yan sandan Isra'ila biyu kan kai wa dan jaridar Turkiyya hari Rundunar ‘yan sandan Isra’ila ta dauki mataki domin hukunta jami’anta biyu wadanda suka kai hari kan dan jarida mai daukar hoto na kamfanin dillancin labarai na Anadolu. Kafar watsa labarai ta Channel 12 ta Isra’ila ta ruwaito cewa an dakatar da ‘yan sandan daga aiki tun bayan lamarin. ‘Yan sandan sun kai wa dan jaridar hari ne a Alkharouf a lokacin da yake daukar rahoto a wurin Sallar Juma’a kusa da Masallacin Al Aqsa da ke Gabashin Birnin Kudus. Rahoton ya ce matakin da aka dauka kan ‘yan sandan zai ci gaba har zuwa lokacin da za a kammala bincike.