Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Kai-tsaye: Amurka ta hana ba da biza ga 'yan Isra'ila da ake zargi da "tayar da hankali" a Yammacin Gabar Kogin Jordan

Isra'ila ta kwashe kwana 286 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,794 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 89,364, kana sama da mutum 10,000 na binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. 2101 GMT — Amurka ta hana ba da biza ga 'yan Isra'ila da ake zargi da "tayar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
Kai-tsaye: Amurka ta hana ba da biza ga 'yan Isra'ila da ake zargi da "tayar da hankali" a Yammacin Gabar Kogin Jordan
De un vistazo

Isra'ila ta kwashe kwana 286 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,794 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 89,364, kana sama da mutum 10,000 na binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. 2101 GMT — Amurka ta hana ba da biza ga 'yan Isra'ila da ake zargi da "tayar...

Isra'ila ta kwashe kwana 286 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,794 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 89,364, kana sama da mutum 10,000 na binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. 2101 GMT — Amurka ta hana ba da biza ga 'yan Isra'ila da ake zargi da "tayar da hankali" a Yammacin Gabar Kogin Jordan Amurka ta sanar da wasu sabbin takunkumin hana biza ga Isra'ilawan da suka tayar da "tarzoma" a kan Falasdinawa a yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye, tana mai kira ga Isra'ila da ta dauki mataki kan wadannan mutane. Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Matthew Miller ya shaida wa manema labarai cewa "Wannan lamari ne game da ƙaruwar tashe-tashen hankula da muka gani cikin bakin ciki a cikin 'yan watannin da suka gabata da kuma bukatar Isra'ila ta ƙara himma wajen daukar mataki a kan mutanen da suke aikata hakan." Matakan sun hana wasu 'yan Isra'ila da 'yan'uwansu shiga Amurka. Miller ya ce gwamnatin Isra'ila ta dauki wasu matakai na murkushe tashe-tashen hankula a Yammacin Gabar Kogin Jordan, kamar kama wasu masu aikata laifuka. "Amma wadannan matakan ba su isa ba," in ji shi. Daga cikin wadanda wannan sabon takunkumin ya shafa har da tsohon sojan Isra'ila Elor Azaria, wanda aka yanke masa hukuncin daurin watanni tara a gidan yari saboda harbi da kashe wani Bafalasdine da ya ji rauni a shekarar 2016. 2230 GMT — Rasha ta ce Iran da Lebanon da Hizbullah ba sa son yaƙi da Isra'ila Babban jami'in diflomasiyyar Rasha ya ce kungiyar Hizbullah ta Lebanon da Iran da gwamnatin Lebanon ba sa son "yaƙi mai cike da rudani - kuma akwai shakkun cewa wasu mutane a Isra'ila na kokarin cimma hakan." Sergey Lavrov ya shaida wa taron manema labarai na Majalisar Dinkin Duniya cewa, Rasha na yin duk mai yiwuwa don kwantar da hankula. Lavrov ya ce gwamnatin da ta gabata ta Iran da kuma sabon shugaban kasar "suna nuna wani matsayi da ke nuna cewa Iran ba ta da sha'awar ci gaba." Ba tare da ba da suna ba, Lavrov ya ce manazarta a Amurka da Turai sun ce "ruruwar rikicin kamar yadda abubuwan da ke faruwa a zahiri suka nuna, wani abu ne da Isra'ila ke sha'awarsa." Lavrov ya kara da cewa, "Hizbullah ta kasance mai kamun kai matuka a cikin ayyukanta, kuma shugabanta Hassan Nasrallah ya ba da jawabai da dama wadanda suka tabbatar da wannan matsayi." “Duk da haka, yana jin cewa ana yunkurin ta da musu hankali da kuma tunzura su cikin wani cikakken salon tsokana,” in ji shi.