Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Kai-tsaye: Amurka ta goyi bayan mamayar Isra'ila a Lebanon yayin da ake ci gaba da kai hare-hare Beirut

Yakin kisan kare dangi na Isra'ila na kwanaki 364 a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 41,788. Hare-haren da Isra'ila ta kai a Lebanon kuwa tun daga Oktoban shekarar 2023 ya yi sanadin mutuwar mutum 1,974 tare da watsa mutum miliyan 1.2. Juma'a 4 ga Oktoban 2024 2100 GMT — Gwamnatin Biden ta...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:13
Kai-tsaye: Amurka ta goyi bayan mamayar Isra'ila a Lebanon yayin da ake ci gaba da kai hare-hare Beirut
Bu haberde ne var?

Yakin kisan kare dangi na Isra'ila na kwanaki 364 a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 41,788. Hare-haren da Isra'ila ta kai a Lebanon kuwa tun daga Oktoban shekarar 2023 ya yi sanadin mutuwar mutum 1,974 tare da watsa mutum miliyan 1.2. Juma'a 4 ga Oktoban 2024 2100 GMT — Gwamnatin Biden ta...

Yakin kisan kare dangi na Isra'ila na kwanaki 364 a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 41,788. Hare-haren da Isra'ila ta kai a Lebanon kuwa tun daga Oktoban shekarar 2023 ya yi sanadin mutuwar mutum 1,974 tare da watsa mutum miliyan 1.2. Juma'a 4 ga Oktoban 2024 2100 GMT — Gwamnatin Biden ta yi imanin cewa ya dace Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare ta kasa da ta sama kan kasar Lebanon a halin yanzu, in ji kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Matthew Miller, duk da cewa ya amince da hatsarin mamaye Lebanon din ya zarce manufofin Isra'ila a halin yanzu. Isra'ila ta aike da dakaru zuwa kudancin Lebanon a wannan makon bayan wani ƙazamin hari ta sama da aka kai tsawon makwanni biyu a cikin wani mummunan rikici da ya janyo Iran da kuma hadarin saka Amurka. Da yake magana a wani taron manema labarai a jiya Alhamis, Miller ya ce yanayin duk rikice-rikicen, ba za a iya tantance shi ba, don haka ba zai yiwu a fadi tsawon lokacin da Isra'ila za ta dauka ba wajen cimma burin da ta bayyana na kawar da ababen more rayuwa na Hezbollah a kudancin Lebanon, tare da ba da dama domin mayar da ‘yan Isra’ila da aka kora daga gidajensu da ke kan iyaka ta hanyar harba rokoki tsawonawatanni. 2130 GMT — Isra'ila ta kashe mutum 37 a Lebanon cikin sa'o'i 24 Sanarwar da Ma'aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta fitar ta ce Isra'ila ta kashe akalla mutum 37 tare da jikkata wasu 151 a hare-haren da ta kai a fadin kasar Lebanon cikin sa'o'i 24 da suka gabata. A halin da ake ciki kuma, makami mai linzamin na Isra'ila ya kai hari a gefen filin jirgin saman Beirut, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito. Har ila yau Isra'ila ta kai hare-hare a yankunan kudancin Beirut "sau 11 a jere", in ji kamfanin dilancin labaran AFP, yana mai cewa an ji ƙarar jiniya kuma gine-gine sun girgiza a babban birnin Lebanon.