Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Kai-tsaye: Amurka ta ce har yanzu ana jiran martanin Hamas kan yarjejeniyar tsagaita wuta

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kwana na 241 inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,550 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — sannan mutum 82,959 sun jikkata, a cewar jami'ai. 0211 GMT — Amurka ta ce har yanzu ana dakon martanin Hamas kan yarjejeniyar tsagaita wuta Ana ci gaba da dakon...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Amurka ta ce har yanzu ana jiran martanin Hamas kan yarjejeniyar tsagaita wuta
Kwa muhtasari

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kwana na 241 inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,550 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — sannan mutum 82,959 sun jikkata, a cewar jami'ai. 0211 GMT — Amurka ta ce har yanzu ana dakon martanin Hamas kan yarjejeniyar tsagaita wuta Ana ci gaba da dakon...

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kwana na 241 inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,550 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — sannan mutum 82,959 sun jikkata, a cewar jami'ai. 0211 GMT — Amurka ta ce har yanzu ana dakon martanin Hamas kan yarjejeniyar tsagaita wuta Ana ci gaba da dakon martanin ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta Hamas kan ƙudirin tsagaita wuta na shugaban Amurka Joe Biden, kamar yadda mashawarcin Fadar White House kan harkokin tsaro Jake Sullivan ya shaida wa manema labarai. "Muna jiran martani daga Hamas" ta hannun masu shiga tsakani na Qatar, in ji Sullivan. Sullivan ya ƙara da cewa daraktan CIA Bill Burns zai kasance a Doha don tuntubar masu shiga tsakani na Qatar kan shawarar tsagaita wuta a Gaza. Qatar dai na shiga tsakani kan Gaza tsakanin Isra'ila da Hamas. Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ci gaba da kasancewa cikin rudani kuma yana ganin Biden ya yi ɓangaranci a cikin shawarar da ya bayar, yayin da abokansa masu tsattsauran ra'ayi ke ƙin duk wata yarjejeniya da Hamas. Sun yi barazanar karya gwamnatin hadin gwiwa da Netanyahu idan ya amince da yarjejeniyar Biden. A halin da ake ciki kuma kakakin Hamas ya nanata cewa ba za su iya amincewa da duk wata yarjejeniya ba, sai dai idan Isra'ila ta bayyana aniyarta "ƙarara" a kan yarjejeniyar tsagaita wuta da ficewa daga Gaza da ta yi wa ƙawanya. 2000 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 19 a Gaza Likitocin Falasdinawa sun bayyana cewa, hare-haren bama-bamai da na sama da Isra'ila ta kai sun kashe akalla mutum 19 a tsakiya da kudancin Gaza ciki har da 'yan sanda biyu da ke taimakawa wajen kare kai agajin jinƙai a kudancin birnin Rafah. Mutum 17 daga cikin waɗanda aka kashe ɗin sun rasa rayukansu ne a wasu hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai kan sansanonin Bureij da Maghazi da kuma birnin Deir al Balah da ke tsakiyar Gaza, kuma da sanyin safiyar Larabar nan tankokin Isra'ila sun yi luguden wuta a wani yanki da ke gabashin sansanin Nuseirat, kamar yadda mazauna garin suka bayyana. Wasu sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters ta wata hanyar manhajar tattaunawa cewa sabon bala'in da sojojin Isra’ila suka jawo na haifar da firgici, inda wasu iyalai da ke zaune a Maghazi suka fara tsere wa luguden wuta da tankokin yaki, inda harsashi hudu suka fado kusa da wani asibiti a sansanin.