Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kai-tsaye: Amurka ta buƙaci MDD ta goyi bayan tsagaita wuta na wucin gadi a Gaza don ƴantar da fursunoni

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza - wanda yanzu ya shiga kwana na 152 - ya kashe Falasɗinawa aƙalla 30,631, galibi yara da mata, tare da jikkata mutum 72,043. 0036 GMT — Amurka ta buƙaci MDD ta goyi bayan tsagaita wuta na wucin gadi a Gaza don ƴantar da fursunoni Amurka ta sake yin gyaran fusk...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:13
Kai-tsaye: Amurka ta buƙaci MDD ta goyi bayan tsagaita wuta na wucin gadi a Gaza don ƴantar da fursunoni
A taƙaice

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza - wanda yanzu ya shiga kwana na 152 - ya kashe Falasɗinawa aƙalla 30,631, galibi yara da mata, tare da jikkata mutum 72,043. 0036 GMT — Amurka ta buƙaci MDD ta goyi bayan tsagaita wuta na wucin gadi a Gaza don ƴantar da fursunoni Amurka ta sake yin gyaran fusk...

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza - wanda yanzu ya shiga kwana na 152 - ya kashe Falasɗinawa aƙalla 30,631, galibi yara da mata, tare da jikkata mutum 72,043. 0036 GMT — Amurka ta buƙaci MDD ta goyi bayan tsagaita wuta na wucin gadi a Gaza don ƴantar da fursunoni Amurka ta sake yin gyaran fuska a cikin wani daftarin ƙudiri na Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don goyan bayan "tsagaita wuta nan da nan na kusan makonni shida a Gaza tare da sakin dukkan wadanda aka yi garkuwa da su," a cewar labarin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani. Bita ta uku ta rubutun - wacce da farko Amurka ta gabatar makonni biyu da suka gabata - yanzu tana nuna kaifafan maganganun da Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris ta yi. Daftarin farko na Amurka ya nuna goyon baya ga "tsagaita wuta na wucin gadi" a cikin kisan gillar da Isra'ila ta yi a yankin Falasdinawa da ta yi wa ƙawanya. Amurka na son duk wani goyon bayan kwamitin sulhu na tsagaita wuta ya kasance yana da alaka da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza. 0123 GMT — Amurka ta harbo makami mai linzami da jirage marasa matuƙa da Houtji suka harba Wani jirgin ruwa na Amurka ya harbo jirage marasa matuka da makami mai linzami da 'yan Houthi na Yaman suka harba a cikin Bahar Maliya, in ji jami'an Amurka, a daidai lokacin da sojojin ruwan Indiya suka fitar da hotunansu na yadda suka kashe gobarar da ta kama a cikin wani jirgin ruwan kwantena da 'yan Houthi suka fara kai wa hari. Harin na Houthi ya hada da jirage marasa matuka masu dauke da bama-bamai da makami mai linzami guda daya na kakkabo jiragen ruwa, in ji rundunar sojin Amurka. Daga baya Amurka ta kai wani hari ta sama, inda ta lalata makami mai linzami guda uku da jiragen ruwa marasa matuka guda uku masu dauke da bama-bamai, in ji rundunar ta tsakiya.