Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe fiye da shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,409. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ƙaɗdamar a Lebanon a Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,350 da raba miliyan 1.2 da muhallansu. Alhamis, 17 ga Oktoban 2024 0300 GMT — Sojojin Amurka sun kai hari a wasu wuraren ajiyar makamai na Houthi a Yemen, in ji manyan jami’an Amurka. "Wannan wani nuni ne na musamman na ikon Amurka na kai hari kan wuraren da abokan hamayyarmu ke samun mafaka, komai ɓuyan da za su yi a karkashin kasa, komai taurarewar su, ko kuma kangarewar su," in ji Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin a cikin wata sanarwa ranar Alhamis. "Aikin da sojojin saman Amurka suka ya nuna yadda Amurka za ta iya kai hari a duniya don daukar mataki kan irin wadannan wurare idan ya kama, kowane lokaci, a ko ina." Wani babban jami'in tsaron Amurka ya shaida wa ABC News cewa, "Rundunar sojin Amurka ta kai hare-hare da dama a kan wuraren ajiyar makamai na Houthi da ke samun goyon bayan Iran a yankunan da ke karkashin ikon Houthi a Yemen." Karin bayani ???? 2340 GMT — Isra’ila ta sake jefa bama-bamai a Lebanon, ta kashe magajin garin Nabatiyeh Isra'ila ta kai hare-hare da dama a Lebanon, inda ta kashe wani magajin gari, da ruguza gine-gine tare da haddasa barna a yankuna da dama na kudancin kasar. Rundunar sojin Isra'ila ta ce jiragen yakinta sun kai hari kan wasu wuraren da kungiyar Hezbollah take a kudancin birnin Nabatiyeh na kasar Lebanon. Ma'aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta ce mutum 16 ne suka mutu sannan wasu 52 suka jikkata sakamakon harin da aka kai kan wasu gine-ginen kananan hukumomi biyu. Akalla mutum shida ne suka mutu a wasu hare-haren kamar yadda jami’ai da rahotanni suka bayyana. Magajin garin Nabatiyeh na cikin wadanda suka mutu, kamar yadda wani jami'in yankin ya shaida wa kamfanin dilancin labaran AFP, ya kuma kara da cewa hare-haren "ya zama wani nau'i na wuta".
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Kai-tsaye: Amurka ta ƙaddamar da jerin hare-haren sama a kan 'yan Houthi a fadin Yemen
Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe fiye da shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,409. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ƙaɗdamar a Lebanon a Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,350 da raba miliyan 1.2 da muhallansu. Alhamis, 17 ga Oktoban 2024 0300 GMT — Sojojin...

At a glance
Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe fiye da shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,409. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ƙaɗdamar a Lebanon a Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,350 da raba miliyan 1.2 da muhallansu. Alhamis, 17 ga Oktoban 2024 0300 GMT — Sojojin...
