Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Kai-tsaye: Amurka na tattaunawa a kan yaƙin Gaza a yayin da dakarun Isra'ila suka sace Falasɗinawa da dama daga Jenin

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na huɗu— bayan Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 47,161 a yankin — sannan mahukuntan Tel Aviv sun ci gaba da kai farmaki a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan. Alhamis, 23 ga Janairu, 2025 2100 GMT — Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi mag...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Amurka na tattaunawa a kan yaƙin Gaza a yayin da dakarun Isra'ila suka sace Falasɗinawa da dama daga Jenin
Kwa muhtasari

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na huɗu— bayan Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 47,161 a yankin — sannan mahukuntan Tel Aviv sun ci gaba da kai farmaki a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan. Alhamis, 23 ga Janairu, 2025 2100 GMT — Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi mag...

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na huɗu— bayan Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 47,161 a yankin — sannan mahukuntan Tel Aviv sun ci gaba da kai farmaki a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan. Alhamis, 23 ga Janairu, 2025 2100 GMT — Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi magana da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu domin jaddada goyon bayan Washington a gare su, sannan mutanen biyu sun tattauna game da Iran da kuma Isra'ila da ake garkuwa da su a Gaza, a cewar Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka. Wannan shi ne karon farko da Rubio ya yi magana da jami'an Isra'ila tun bayan da aka rantsar da Donald Trump ranar Litinin. Trump da mutumin da ya gabace shi, tsohon shugaban ƙasa Joe Biden, sun bayyana goyon yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza. Rubio ya bayyana muhimmancin matakin " Amurka na ci gaba da goyon bayan Isra'ila a matsayin babban abin da Trump ya sanya a gaba," in ji wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar. Rubio ya shaida wa Netanyahu cewa Washington za ta ci gaba da goyon bayan Isra'ila "ba tare da gajiyawa ba" domin ganin an ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza. "Kazalika Sakataren Harkokin Wajen ya miƙa fatansa na ganin an daƙile duk wata barazana da ke fitowa daga Iran da kuma tabbatar da zaman lafiya," a cewar sanarwar. 2000 GMT — Dakarun Isra'ila sun sace ƙarin Falasɗinawa bakwai Dakarun mamaya na Isra'ila sun sace Falasɗinawa aƙalla bakwai daga biranen Jenin da Jericho na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, kamar yadda kamfanin dillancin WAFA ya ambato wasu majiyoyi suna tabbatawa. "Dakarun mamaya sun yi wa Falasɗinawa huu ƙawanya; mata biyu iyayen wasu Falasɗinawa biyu da dakarun Isra'ila suka kashe a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin ," in ji kamfanin dillancin labaran na Falasɗinu. Dakarun Isra'ila sun kai samame a birnin Jericho, lamarin da ya kai ga arangama, a cewar WAFA, inda kamfanin labaran ya ƙara da cewa dakarun an Isra'ila sun sace matasa biyu a yankin Silwan na Birnin Ƙudus.