Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Kai-tsaye: Algeria za ta gabatar wa Kwamitin Tsaro na MDD ƙudirin kira a tsagaita wuta a Gaza

Isra'ila ta kwashe kwana 229 tana kai hare-hare a Gaza abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 36,096 — kaso 71 daga cikinsu jarirai, mata da yara — sannan ta jikkata mutum 81,136, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 2300 GMT — Ƙasar Aljeriya ta yaɗa wani ƙuduri a M...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
Kai-tsaye: Algeria za ta gabatar wa Kwamitin Tsaro na MDD ƙudirin kira a tsagaita wuta a Gaza
De un vistazo

Isra'ila ta kwashe kwana 229 tana kai hare-hare a Gaza abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 36,096 — kaso 71 daga cikinsu jarirai, mata da yara — sannan ta jikkata mutum 81,136, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 2300 GMT — Ƙasar Aljeriya ta yaɗa wani ƙuduri a M...

Isra'ila ta kwashe kwana 229 tana kai hare-hare a Gaza abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 36,096 — kaso 71 daga cikinsu jarirai, mata da yara — sannan ta jikkata mutum 81,136, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 2300 GMT — Ƙasar Aljeriya ta yaɗa wani ƙuduri a Majalisar Dinkin Duniya da ke neman a tsayar da yaƙin da ake yi a Gaza nan-take da kuma umarnin Isra’ila ta tsayar da kutsen sojoji a kudancin birnin Rafah ba tare da jinkiri ba. Ƙudirin wanda kamfanin dillacin labarai na AP ya samu ya kuma buƙaci duka ɓangarorin da ke yaƙin su mutunta tsagaita wutar. Ya kuma yi kira da a sako gaba ɗaya mutanen da aka yi garkuwa da su lokacin da Hamas ta kai hari sansanin sojan Isra'ila da kuma matsugunan Yahudawa a kudancin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba. Haka kuma ƙudirin ya nemi a yi aiki da ƙudurce-ƙudurce na baya da suka yi kira a buɗe duka iyakokin yankin da kuma barin kayan agaji su isa ga mutane miliyan 2.4 da suke tsananin buƙatar abinci da sauran agaji. Matakin da ake shirin gabatarwa ya ce "mummunan yanayin da ake ciki a Gaza yana barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin da kuma duniya baki ɗaya." Ƙudirin ya ce "Lallai Isra'ila ta dakatar da harin da sojojinta ke kaiwa da ma duk wani mataki a Rafah." Ya kuma yi Allah-wadai da "kisan kan mai-uwa-da-wabi da fararen-hula ciki har da mata da yara da wuraren amfanin fararen hula" ya kuma jaddada cewa majalisar ta nemi duka ɓangarorin su yi aiki da dokokin duniya da suka buƙaci kare fararen-hula. Amurka tana kare ƙawarta Isra'ila a lokuta da dama, sannan ta hau kujerar na-ƙi a ƙudurori da dama da ke neman a tsagaita wuta a Gaza.