Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Kai-tsaye: Agaji 'ba ya isa wurin mutanen da ke Gaza, yara suna cikin masifar yunwa' — MDD

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 36,224 - galibinsu mata da yara da jarirai - a hare-haren da ta kwashe kwana 237 tana kai wa Gaza, kana ta jikkata sama da mutum 81,777 237, yayin da kuma aƙalla mutum 10,000 ke binne a ɓaraguzan gine-gine. 1050 GMT — Agaji 'ba ya isa wurin mutane' da ke Gaza...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Agaji 'ba ya isa wurin mutanen da ke Gaza, yara suna cikin masifar yunwa' — MDD
At a glance

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 36,224 - galibinsu mata da yara da jarirai - a hare-haren da ta kwashe kwana 237 tana kai wa Gaza, kana ta jikkata sama da mutum 81,777 237, yayin da kuma aƙalla mutum 10,000 ke binne a ɓaraguzan gine-gine. 1050 GMT — Agaji 'ba ya isa wurin mutane' da ke Gaza...

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 36,224 - galibinsu mata da yara da jarirai - a hare-haren da ta kwashe kwana 237 tana kai wa Gaza, kana ta jikkata sama da mutum 81,777 237, yayin da kuma aƙalla mutum 10,000 ke binne a ɓaraguzan gine-gine. 1050 GMT — Agaji 'ba ya isa wurin mutane' da ke Gaza, 'yara suna cikin masifar yunwa' — MDD Ofishin bayar da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya da Hukumar Lafiya ta (WHO) sun yi gargaɗi cewa agaji "ba ya isa wurin mutanen da ke" Gaza, kuma hakan ya sa yara sun faɗa cikin "bala'in yunwa." "Tabbas ba ba sa samun agajin da suke matuƙar buƙata domin kauce wa kamuwa da tamowa," a cewar Jens Laerke, kakakin Ofishin bayar da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya, a wurin wani taron MDD a Geneva. Da yake bayani game da yiwuwar Isra'ila ta ƙwace Mashigin Philadelphi, Laerke ya ce: "Ƙarin kai hare-hare ba zai taimaka wa aikin bayar da agaji ba." Ya ƙara da cewa abu ne mai "wahala a yi hasashen" yadda hakan zai shafi aikin bayar da agaji bak ɗaya, idan aka yi la'akari da "yadda yanayi yake sauyawa" a yankin inda dakarun tsaro suke motsawa daga wani waje zuwa wani. "Muna so a daina kai hare-hare baki ɗaya. Hakan ne kawai zai ba mu damar gudanar da ayyukanmu yadda suka kamata." 2238 GMT —Wani harin haɗin-gwiwa na Amurka da Birtaniya ya kashe mutum biyu a Yemen Sojojin Amurka da na Birtaniya sun sanar cewa sun kai hare-hare kan mayaƙan Houthi da ke Yemen. Ranar Alhamis kafar watsa labarai ta Houthi ta tabbatar da kisan aƙalla mutum biyu a hare-haren. Ma'aikatar tsaron Birtaniya ta ce an kai hare-haren na haɗin-gwiwa ne a wurare uku a birnin Hodeidah da ke gaɓar Bahar Maliya. Gidan talbijin na Al Masirah wanda ƙungiyar Houthi take gudanar da shi ya ruwaito cewa an kashe aƙalla mutum biyu sannan aka jikkata mutum 10 a hare-haren da aka kai a wani gini na gidan rediyo a lardin Al-Hawk na birnin Hodeidah. Jirgin yaƙin Birtaniya samfurin RAF Typhoons yana cikin jiragen da suka kai hari kan mayaƙan Houthi a Yemen. / Hoto: X 0340 GMT — 'Yan majalisa na jam'iyyun adawa a Faransa sun yi kira a ƙaurace wa wani gidan talabijin saboda ya yi hira da Netanyahu 'Yan majalisar dokokin Faransa na jam'iyyun adawa sun yi kira a ƙaurace wa gidan talbijin na LCI bayan ya watsa wata hira da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ranar Alhamis. An watsa hirar ce a wani shiri mai suna Le 20h de Darius Rochebin, a talbijin na LCI , mallakin gamayyar kamfanoni ta TF1 Group. 'Yan siyasa na jam'iyyun adawa da masu amfani da soshiyal midiya sun nuna matuƙar rashin jin daɗinsu kan watsa hirar, inda suka bayyana Netanyahu a matsayin "mai kisan kai," "mai kisan kiyashi" kuma "wanda ya aikata laifukan yaƙi."