Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Kai-tsaye: Adadin wadanda suka mutu a Gaza ya zarce 34,700 yayin da Isra'ila ta fara kai farmaki Rafah

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 213, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,683 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,018 ne suka jikkata. 1224 GMT — Adadin wadanda suka mutu a Gaza ya zarce 34,700 yayin da Isra'ila ta fara kai far...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
Kai-tsaye: Adadin wadanda suka mutu a Gaza ya zarce 34,700 yayin da Isra'ila ta fara kai farmaki Rafah
De un vistazo

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 213, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,683 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,018 ne suka jikkata. 1224 GMT — Adadin wadanda suka mutu a Gaza ya zarce 34,700 yayin da Isra'ila ta fara kai far...

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 213, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,683 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,018 ne suka jikkata. 1224 GMT — Adadin wadanda suka mutu a Gaza ya zarce 34,700 yayin da Isra'ila ta fara kai farmaki Rafah Akalla Falasdinawa 34,735 aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa Gaza tun a watan Oktoban bara, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza. Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu mutum 78,108 kuma sun jikkata a yaƙin. Sanarwar ta ce "Hare-haren Isra'ila sun kashe mutum 52 tare da jikkata wasu 90 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata." Ya kara da cewa "har yanzu mutane da dama na maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine da kuma kan tituna yayin da masu ceto suka kasa kai musu ɗauki." 0754 GMT — Kwashe mutane da Isra'ila ke yi daga Rafah na iya jawo mummunar ta'azzarar rikicin — Hamas Babban jami'in Hamas Sami Abu Zuhri ya ce kwashe mutane da Isra'ila ke yi daga Rafah gabanin hare-haren da ake sa ran za ta ƙaddamar wani "mummunan lamari ne da ka iya ta'azzara yaƙin da ake yi, kuma zai jawo ɗumbin matsaloli." Kazalika jami'an Hamas sun yi ikirarin cewa matakin kwashe Falasdinawa daga Rafah zai jawo tsaiko wajen sasantarwar sakin mutanen da ake garkuwa da su. Sojojin Isra'ila sun fara kwashe mutane da ga yankunan da ke kusa da kan iyakar gabashin Rafah, gabain wani farmaki ta ƙasa da ake sa ran za a kai a birnin Falasɗinun da ke kudancin Gaza a yau. Duk da ƙaruwar adawa da yake fuskanta daga ƙasashen duniya, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin kai farmaki Rafah, yankin da ke ɗauke da Falasɗinawa fiye da miliyan 1.4 da ke neman mafaka a wajen. 0615 GMT — Hezbollah ta Labanon ta ce ta harba gomman rokoki a wani sansanin sojon Isra'ila Ƙungiyar Hezbollah ta Labanon da ke samun goyon bayan Iran ta ce ta harba gomman makaman rokokin Katyusha a wani sansanin sojin Isra'ila da ke Tuudan Golan da aka mamaye, a wani martani ga wani hari da Isra'ilan ta kai gabashin Labanon. Mayaƙan Hezbollah sun ƙaddamar da "gomman hare-haren makaman rokoki na Katyusha" da nufin samun hedikwatar sansanin soji da ke Tuddan Golan," kamar yadda ƙungiyar ta faɗa a wata sanarwa, tana mai cewa "harin martanin ne kan harin da maƙiya suka kai yankin Bekaa."