Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 342, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,118 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,125 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla ƙarin Falasɗinawa 34 a Gaza, abin da ya kai adadin waɗanda suka mutu tun daga 7 ga Oktoba zuwa 41,118, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta yankin. Wata sanarwar ma'aikatar ta ƙara da cewa an jikkata fiye da wasu mutanen 95,125 a hare-haren da ake ci gaba da kaiwa. "A cikin sa'o'i 24, Sojojin Israi'ila sun kashe mutane 34 sun kuma jikkata wasu 96 a kashe-kashe na ƙare dangi da suke yi wa iyalai," a cewar ma'aikatar. Ta ƙara da cewa "Mutane da dama har yanzu suna kwance a ƙasan ɓaraguzai da kuma gefen hanyoyi kasancewar masu aikin ceto ba sa iya kaiwa gare su." 0843 GMT — Turkiyya za ta binciki kisan da aka yi wa mai ayuakan jin ƙai 'yar gwagwarmaya a Gaɓar Yamma Turkiyya na binciken kisan da aka yi wa Ba'amurkiya kuma Baturkiya 'yar gwagwarmaya Aysenur Ezgi Eygi yayin wata zanga-zanga a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da sojojin Isra'ila suka mamaye, kamar yadda ministan shari'a ya bayyana, yana mai cewa Ankara za ta matsa wa Majalisar Ɗinkin Duniya kan ta ɗauki mataki nan take. "Turkiyya ta fara bincike," a cewar Ministan Shari'a Yilmaz Tunc. "Za mu yi aiki don tabbatar da cewa Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya na Musamman kan Kisan Zalinci ya ɗauki mataki nan-take, sannan a kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa ya kuma fitar da rahoto," a cewarsa.
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Kai-tsaye: Adadin waɗanda aka kashe a Gaza ya kai 41,118 yayin da Isra'ila ke ci gaba da kashe Falasɗinawa
Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 342, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,118 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,125 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla ƙarin Falasɗinawa 34 a...

Bu haberde ne var?
Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 342, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,118 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,125 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla ƙarin Falasɗinawa 34 a...
