Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,227. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ƙadamar a Lebanon tun Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,306 da raba miliyan 1.2 da muhallansu. Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024 2316 GMT — Adadin mutanen da suka mutu sakamakon wani hari ta sama da Isra'ila ta kai a wata makaranta a tsakiyar Gaza ya ƙaru zuwa 22, a cewar ofishin watsa labarai na gwamnatin yankin. Ya ƙara da cewar sojojin Isra'ila "suna sane cewa dubban mata da yara da aka kora daga gidajensu suna samun mafaka a makarantar ta Mufti amma suka kai mata hari da bama-bamai." Ƙarin bayani ???? 0212 GMT — Amurka ta nemi Isra'ila a bi hanyar diflomasiyya kan yaƙin Lebanon Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin ya ce akwai buƙtatar Isra'ila ta daina amfani da ƙarfin soji kana ta rungumi hanyar diflomasiyya a yaƙin da take yi a Lebanon. Da yake magana ta wayar tarho da Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant, Austin ya ce ya ika ta'aziyyarsa bisa mutuwar sojojin Isra'ila a wani hari na jirgi mara matuƙi da Hezbollah ta kai musu. "Na jaddada buƙatar tabbatar da tsaron lafiyar (Dakarun Wanzar da Tsaro na MDD a Lebanon) UNIFIL da Sojojin Lebanon da kuma buƙatar mayar da hankali kan sulhu ta hanyar diflomasiyya da daina amfani da ƙarfin soji," in ji shi a saƙn da ya wallafa a shafin X. 2142 GMT — Isra'ila ta ce harin da Hezbollah ta kai da jirgi mara matuƙi ya kashe sojojinta 4 Rundunar sojojin Isra'ila ta ce sojojinta huɗu sun mutu sakamakon harin da Hezbollah ta kai da jirgi mara matuƙi a sansaninsu da ke kudancin Haifa. "An kashe sojoji huɗu na IDF a harin, sannan guda bakwai sun yi mummunar jikkata,"a cewar wata sanarwa da rundunar sojojin ta fitar.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Kai-tsaye: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da Isra'ila ta kai a wata makaranta a Gaza ya ƙaru zuwa 22
Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,227. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ƙadamar a Lebanon tun Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,306 da raba miliyan 1.2 da muhallansu. Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024 2316 GMT — Adadin m...

At a glance
Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,227. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ƙadamar a Lebanon tun Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,306 da raba miliyan 1.2 da muhallansu. Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024 2316 GMT — Adadin m...
