Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Kai-tsaye: Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Lebanon ya kai 3,670

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 415 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,176 tare da jikkata fiye da mutum 104,473. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 3,670 tun daga watan Oktoban 2023. Lahadi, 24 ga Nuwamba, 2024 2009 GMT — Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙal...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:13
Kai-tsaye: Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Lebanon ya kai 3,670
En bref

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 415 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,176 tare da jikkata fiye da mutum 104,473. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 3,670 tun daga watan Oktoban 2023. Lahadi, 24 ga Nuwamba, 2024 2009 GMT — Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙal...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 415 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,176 tare da jikkata fiye da mutum 104,473. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 3,670 tun daga watan Oktoban 2023. Lahadi, 24 ga Nuwamba, 2024 2009 GMT — Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla ƙarin mutum 25 a faɗin Lebanon a kwanaki uku da suka gabata, abin da ya kai jumullar mutanen da aka kashe tun daga Oktoban bara zuwa 3,670, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon. A wata sanarwa, ma'aikatar ta ƙara da cewa an kuma jikkata wasu mutane 58, abin da ya kai adadin waɗanda aka jikkata zuwa 15,413 tun daga Oktoban 2023. Ƙarin labarai???? 2208 GMT — Jiragen Isra'ila marasa matuƙi sun kashe ma'aikatan lafiya biyu, sun jikkata 4 a yankin Tyre na kudancin Lebanon Jiragen Isra'ila marasa matuƙa sun bi ma'aikatan lafiya a yankin Tyre na kudancin Lebanon, inda suka kashe biyu suka kuma jikkata huɗu daga cikinsu. “Wani jirgin Isra'ila mara matuƙi ya nufi tawagarmu mai aikin ceto yayin da suke tafiya garin Ain Baal a gundumar Tyre don aikin ceto na gaggawa," kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon ta bayyana. "Yayin da tawagar ceto to biyu ta tafi wajen da sauri don ceto waɗanda aka jikkata a tawagar farko, ita ma jirgin Isra'ila mara matuki ya kai mata hari, abin da ya janyo shahadar mutum biyu da jikkata mutane huɗu daga tawagogin biyu." 2139 GMT — Hare-haren Isra'ila ta sama sun kashe mutum 20 a tsakiyar Beirut Adadin mutanen da suka mutu a harin jiragen yaƙi da Isra'ila ta kai tsakiyar Beirut ya kai 20, yayin da aka jikkata wasu 66, a cewar Ma'aikatar Lafiya. Kamfanin dillancin labarai na gwamnati na Lebanese National News Agency ya ce harin ya rusa wani gida mai hawa takwas a titin Al-Mamoun a gundumar Basta. Tawagar masu aikin ceto da masu ba da agajin gaggawa suna aiki domin zaƙulo mutane daga ɓaraguzai da kuma taimakon waɗanda suke da sauran numfashi. An gaggauta tafiya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci, wasunsu suna cikin mawuyacin hali.