Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kai-tsaye: Adadin Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe a sansanin Nuseirat ya kai 274

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kwana na 247 inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,801 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — sannan mutum 83,680 sun jikkata, a cewar jami'ai. 1041 GMT — Adadin Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe a sansanin Nuseirat ya kai 274 A yayin da ake ci gaba da j...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:13
Kai-tsaye: Adadin Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe a sansanin Nuseirat ya kai 274
A taƙaice

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kwana na 247 inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,801 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — sannan mutum 83,680 sun jikkata, a cewar jami'ai. 1041 GMT — Adadin Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe a sansanin Nuseirat ya kai 274 A yayin da ake ci gaba da j...

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kwana na 247 inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,801 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — sannan mutum 83,680 sun jikkata, a cewar jami'ai. 1041 GMT — Adadin Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe a sansanin Nuseirat ya kai 274 A yayin da ake ci gaba da jimami a Gaza, adadin Falasɗinawan da Isra’ila ta kashe a sansanin gudun hijira na Nuseirat ya ƙaru zuwa 274, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta tabbatar. A ranar Asabar ne da safe Isra’ila ta kai hari sansanin, inda alƙaluma na baya-bayan nan da ma’aikatar lafiyar ta sanar suka nuna cewa mutum 698 ne suka jikkata. Ƙasashen duniya da ƙungiyoyi sun ta yin Allah wadai da wannan kisan na baya-bayan nan da sojojin Isra’ila suka aikata. 1011 GMT — Kai-tsaye: MDD ta nuna damuwa kan harin Isra'ila da ya kashe sama da mutum 200 a rana guda Shugaba Hukumar Bayar da Agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna damuwarsa dangane da irin harin da Isra’ila ta kai a sansanin gudun hijira na Nuseirat wanda ke a tsakiyar Gaza, wanda ya ja aƙalla mutum 210 suka rasu sannan sama da 400 suka jikkata. “A yau, sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat shi ne cibiyar bala'i da farar hular Gaza ke ci gaba da fuskanta,” in ji shi. Hotunan irin yadda aka samu mace-mace bayan harin Isra’ila na ƙara nuna hujjar cewa Isra’ila na ci gaba da yaƙin nan a kullu, kamar yadda Martin Griffiths ya bayyana a wata sanarwa. Griffiths ya sake nanata cewa babu inda ke da aminci a Gaza kuma kula da lafiya a yankin da aka yi wa kawanya "na cikin mawuyacin hali."