Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

KAI-TSAYE: Adadin Falasdinawa da suka mutu ya kai 26,900 a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 117 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 26,751 sannan suka jikkata mutum 65,636, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 0944 GMT — Adadin Falasdinawa da suka mutu ya kai 26,900 a hare-haren da Isra'ila...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:13
KAI-TSAYE: Adadin Falasdinawa da suka mutu ya kai 26,900 a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza
A taƙaice

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 117 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 26,751 sannan suka jikkata mutum 65,636, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 0944 GMT — Adadin Falasdinawa da suka mutu ya kai 26,900 a hare-haren da Isra'ila...

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 117 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 26,751 sannan suka jikkata mutum 65,636, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 0944 GMT — Adadin Falasdinawa da suka mutu ya kai 26,900 a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce akalla mutum 26,900 ne aka kashe a yankin Falasdinawa da aka yi wa ƙawanya tun bayan barkewar yakin da Isra'ila ke yi a ranar 7 ga watan Oktoba. Rahoton na baya-bayan nan ya hada da mutuwar mutum 150 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, in ji sanarwar ma'aikatar, ta kuma kara da cewa mutum 65,949 ne suka jikkata a Gaza tun bayan barkewar fadan. 0903 GMT — Isra'ila ta ƙara rasa sojojinta uku a Gaza Rundunar Sojin Isra’ila ta sanar da cewa ta rasa ƙarin sojojinta uku a yaƙin da take yi da Falasɗinawa a Zirin Gaza, kamar yadda rundunar sojin ƙasar ta sanar a ranar Laraba. A wata sanarwa daga shafin jaridar Times of Israel, rundunar sojin ta Isra’ila ta ce akwai sojojinta biyu waɗanda aka ji wa mummunan rauni a kudancin Gaza. Adadin sojojin Isra’ila da aka kashe tun bayan soma wannan yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 560. 0830 GMT — Isra'ila ta umarci Falasɗinawa 88,000 su fice daga yammacin Gaza Isra'ila ta ƙara bayar da wani sabon umarni ga Falasɗinawa akalla 88,000 waɗanda suka rasa muhallansu da ke zaune a yammacin birnin Gaza kan su tashi daga wurin, kamar yadda Hukumar Kula da Ayyukan Jin Kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar. Yankin wanda ya haɗa da sansanin ƴan gudun hijira na Ash Shati, ya kasance wuri da ke da mazauna kusan 300,000 kafin fara yakin. Tun bayan fara wannan yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba Isra'ila ta bai wa mazauna Gaza wa'adi kan su fice daga birnin.