Isra'ila ta jima tana nema Sinwar, inda Tel Aviv take zarginsa da tsara harin Hamas na kan iyaka ranar 7 ga Oktoba. Kafofin watsa labaran Isra'ila sun rawaito cewa an kashe shugaban ofishin siyasa na Hamas Yahya Sinwar a Gaza. Biyu daga cikin gidajen yaɗa labarai na Isra'ila, KAN da N12 News sun ambato jami'an Isra'ila a ranar Alhamis suna cewa Sinwar ya mutu. Babu wani tabbaci a hukumance daga Hamas. Da farko dai rundunar sojin Isra'ila ta ce tana duba yiwuwar kashe Sinwar bayan wani farmaki da ta kai a Gaza kan mayakan gwagwarmayar Falasdinawa uku. An nada Sinwar a matsayin shugaban Hamas bayan kashe tsohon shugaban siyasa na ƙungiyar Ismail Haniyeh a Tehran na Iran a watan Yuli. Sinwar shi ne shugaban Hamas da Isra'ila ta fi nema ruwa a jallo, inda Tel Aviv ta zarge shi da kitsa harin kan iyaka da ƙungiyar ta kai a ranar 7 ga Oktoban bara, wanda ya sa Isra'ila ta ƙaddamar da wani mummunan yakin soji a Gaza wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 45,000 a cewar sanarwar hukumomin lafiya na yankin. Watanni goma da yakin Isra'ila, yankunan Gaza da dama sun zama kango a a loakcin da aka hana shiga da abinci da ruwan sha da magunguna. Rundunar sojin Isra'ila ta ce babu alamun akwai wadanda aka yi garkuwa da su a ginin da aka kashe mutanen uku.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Kafofin labaran Isra'ila sun yi da'awar an kashe shugaban Hamas Yahya Sinwar a harin da aka kai Gaza
Isra'ila ta jima tana nema Sinwar, inda Tel Aviv take zarginsa da tsara harin Hamas na kan iyaka ranar 7 ga Oktoba. Kafofin watsa labaran Isra'ila sun rawaito cewa an kashe shugaban ofishin siyasa na Hamas Yahya Sinwar a Gaza. Biyu daga cikin gidajen yaɗa labarai na Isra'ila, KAN da N12 News sun...

لمحة سريعة
Isra'ila ta jima tana nema Sinwar, inda Tel Aviv take zarginsa da tsara harin Hamas na kan iyaka ranar 7 ga Oktoba. Kafofin watsa labaran Isra'ila sun rawaito cewa an kashe shugaban ofishin siyasa na Hamas Yahya Sinwar a Gaza. Biyu daga cikin gidajen yaɗa labarai na Isra'ila, KAN da N12 News sun...
