Karawar da aka yi mai taken "Knockout Chaos" a Turancin Ingilishi ta ƙayatar da ƴan kallo inda Joshua ya buge Ngannou. Tsohon gwarzon ɗan damben boksin na duniya Anthony Joshua ya doke Francis Ngannou sau uku a zagaye biyu da suka fafata a filin wasa na Kingdom Arena a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya ranar Asabar lamarin da ya ƙara masa tagomashi a fagen boksin. Joshua, ɗan ƙasar Birtaniya da ke da tsatso a Nijeriya ya doke Ngannou, haifaffen ƙasar Kamaru mai shekara 37. Karawar da aka yi mai taken "Knockout Chaos" a Turancin Ingilishi ta ƙayatar da ƴan kallo inda Joshua ya buge Ngannou. Alƙalin wasan ya yi gaggawar shiga tsakanin inda ya tsayar da wasan sannan ya ayyana Joshua a matsayin wanda ya yi nasara bayan ya bubbuge Ngannou. Masu kallon sun yi tsamanin Ngannou zai yi kataɓus a wasan bayan ya doke tsohon gwarzon ɗan wasan boksin Tyson Fury a fafatawar da suka yi a Riyadh a watan Oktoba, amma sai ga shi Joshua ya murƙushe shi.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Joshua ya doke Ngannou a damben boksin da suka fafata a Saudiyya
Karawar da aka yi mai taken "Knockout Chaos" a Turancin Ingilishi ta ƙayatar da ƴan kallo inda Joshua ya buge Ngannou. Tsohon gwarzon ɗan damben boksin na duniya Anthony Joshua ya doke Francis Ngannou sau uku a zagaye biyu da suka fafata a filin wasa na Kingdom Arena a birnin Riyadh na ƙasar Saud...

At a glance