Kanar Alper Gezeravci, tare da tawagar Ax-3, za su tashi zuwa Tashar Sararin Samaniya ranar 18 ga watan Janairu, a cewar Ministan Masana'antu da Fasaha na Turkiyya Mehmet Fatih Kacır. Jirgin sama-jannatin Turkiyya na farko zai tafi Tashar Sararin Samaniya [ISS] da misalin karfe daya da minti goma na dare agogon kasar a ranar 18 ga watan Janairu, a cewar wani babban jami'in kasar da kuma hukumar sararin samaniya ta Amurka NASA. Kanar Alper Gezeravci da tawagarsa za su shiga jirgin sama-jannatin mai suna Axiom Mission 3 [Ax-3] zuwa tashar ta sararin samaniya ta ISS, in ji Ministan Masana'antu da Fasaha na Turkiyya Mehmet Fatih Kacir a sakon da ya wallafa a shafin X ranar Alhamis. "Wannan tafiya mai dimbin tarihi za ta za karfafa gwiwar al'umma mai zuwa da kuma kasancewa wani muhimmin mataki a kimiyyar sararin samaniya ta Turkiyya," a cewar Kacir. Rokar Falcon 9 ta kamfanin SpaceX ce za ta harba tawagar ta Ax-3 a cikin kumbon Dragon cibiyar Kennedy da ke birnin Florida na Amurka zuwa sararin samaniya Ana sa rai kumbon zai sauka a Tashar Sararin Samaniya ranar 19 ga watan Janairu da misalin karfe daya da kwata na rana. Alarmınızı kurmayı unutmayınız. ????️⏰ Fırlatma: 17 Ocak 2024 17:11 (Florida) 18 Ocak 2024 01:11 (Türkiye) Uluslararası Uzay İstasyonu’na Kenetlenme: 19 Ocak 2024 05:15 (Florida) 19 Ocak 2024 13:15 (Türkiye) Türkiye’nin İnsanlı İlk Uzay Misyonu için Türkiye Uzay Ajansı @tuajans … https://t.co/pbtULECyNe pic.twitter.com/HLUV4NBPcJ — Mehmet Fatih KACIR (@mfatihkacir) January 4, 2024 ???? Mission Update: The #Ax3 mission is targeted to liftoff from Launch Complex 39A in Florida no earlier than Jan. 17 at 5:11pm ET. Docking with the @Space_Station is expected for Jan. 19 at ~5:15am ET. NASA is enabling commercial space by supporting private astronaut missions. pic.twitter.com/vildd8PZMM — NASA's Johnson Space Center (@NASA_Johnson) January 4, 2024
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Jirgin sama-jannatin Turkiyya na farko zai tafi Tashar Sararin Samaniya a watan Janairun da muke ciki
Kanar Alper Gezeravci, tare da tawagar Ax-3, za su tashi zuwa Tashar Sararin Samaniya ranar 18 ga watan Janairu, a cewar Ministan Masana'antu da Fasaha na Turkiyya Mehmet Fatih Kacır. Jirgin sama-jannatin Turkiyya na farko zai tafi Tashar Sararin Samaniya [ISS] da misalin karfe daya da minti goma...

لمحة سريعة
Kanar Alper Gezeravci, tare da tawagar Ax-3, za su tashi zuwa Tashar Sararin Samaniya ranar 18 ga watan Janairu, a cewar Ministan Masana'antu da Fasaha na Turkiyya Mehmet Fatih Kacır. Jirgin sama-jannatin Turkiyya na farko zai tafi Tashar Sararin Samaniya [ISS] da misalin karfe daya da minti goma...
