Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Jirgin ƙasan Kaduna-Abuja na Nijeriya ya yi hatsari bayan sauka daga layinsa

Zuwa lokacin wallafa wannan labari dai hukumar kula da layukan dogo ta Nijeriya ba ta ce komai a kan lamarin ba, sannan ba a san musabbabin faruwar hatsarin ba. Jirgin ƙasan da ke zirga-zriga tsakanin Abuja zuwa Kaduna a Nijeriya ya yi hatsari bayan da ya sauka daga layinsa a ranar Talata. Lamari...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
Jirgin ƙasan Kaduna-Abuja na Nijeriya ya yi hatsari bayan sauka daga layinsa
De un vistazo

Zuwa lokacin wallafa wannan labari dai hukumar kula da layukan dogo ta Nijeriya ba ta ce komai a kan lamarin ba, sannan ba a san musabbabin faruwar hatsarin ba. Jirgin ƙasan da ke zirga-zriga tsakanin Abuja zuwa Kaduna a Nijeriya ya yi hatsari bayan da ya sauka daga layinsa a ranar Talata. Lamari...

Zuwa lokacin wallafa wannan labari dai hukumar kula da layukan dogo ta Nijeriya ba ta ce komai a kan lamarin ba, sannan ba a san musabbabin faruwar hatsarin ba. Jirgin ƙasan da ke zirga-zriga tsakanin Abuja zuwa Kaduna a Nijeriya ya yi hatsari bayan da ya sauka daga layinsa a ranar Talata. Lamarin ya faru ne a garin Asham, kamar yadda wani mai amfani da shafin Facebook, Imo Onyekwere ya fara wallafa faruwar lamarin kai-tsaye ta bidiyo a shafinsa . Hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 11 na safe, jim kaɗan bayan tashin jirgin daga Abuja zuwa Kaduna. A cikin bidiyon, ana iya ganin yadda taragun jirgin suka tuntsura, kuma mutane sun taru a wajen suna kallon abin da ya faru da ƙoƙarin aikin ceto, yayin da wasu da suka fi kama da fasinjoji na tsaye cirko-cirko. Hukumar kula da layukan dogo ta Nijeriya, NRC ta ce tuni an tura tawagogin agaji da na jami'an lafiya don kai waɗanda suka jikkata asibiti.