Harin wanda aka kai shi a garin Tinzaouaten da ke kan iyakar Mali da Aljeriya ya yi sanadin mutuwar gawurtaccen ɗan tawayen nan Fahad Ag Almahmoud, kamar yadda gwamnatin ta Mali ta bayyana. Gwamnatin Mali ta sanar da kashe wani babban kwamandan 'yan tawayen Abzinawa da wasu 'yan tawayen a wani hari da jirgi maras matuƙi a arewacin ƙasar. Wani ɗan jaridar kamfanin dillancin labarai na Reuters a garin Tinzaouaten da ke kan iyakar Mali da Aljeriya ya shaida harin da aka kai a garin, wanda ke ƙarƙashin ikon wata haɗaka ta ‘yan tawaye wadda ake kira the Permanent Strategic Framework for the Defence of the People of Azawad (CSP-DPA). “An kashe mayaƙan CSP da dama, ciki har da gawurtaccen nan Fahad Ag Almahmoud,” in ji Chodi Ag, wanda ma’aikaci ne a ma’aikatar watsa labarai ta Mali a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Almahmoud wanda aka fi sani da Gatia, ya kasance tsohon mamba a mayaƙan sa kai da ke goyon bayan gwamnatin Mali, inda daga bisani ya ɓalle ya zama ɗan tawaye a bara. Wata majiya ta soji wadda ba ta so a faɗi sunanta ta bayyana cewa harin da aka kai a Tinzaouaten ya kashe Almahmoud da wasu “shugabannin ‘yan ta’adda”. Sai dai zuwa yanzu sojojin Mali ba su yi ƙarin bayani a game da wannan harin ba.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Jirgi maras matuƙi ya kashe wani babban kwamandan 'yan tawayen Abzinawa a Mali — Hukumomi
Harin wanda aka kai shi a garin Tinzaouaten da ke kan iyakar Mali da Aljeriya ya yi sanadin mutuwar gawurtaccen ɗan tawayen nan Fahad Ag Almahmoud, kamar yadda gwamnatin ta Mali ta bayyana. Gwamnatin Mali ta sanar da kashe wani babban kwamandan 'yan tawayen Abzinawa da wasu 'yan tawayen a wani ha...

Harin wanda aka kai shi a garin Tinzaouaten da ke kan iyakar Mali da Aljeriya ya yi sanadin mutuwar gawurtaccen ɗan tawayen nan Fahad Ag Almahmoud, kamar yadda gwamnatin ta Mali ta bayyana. Gwamnatin Mali ta sanar da kashe wani babban kwamandan 'yan tawayen Abzinawa da wasu 'yan tawayen a wani ha...
