Ƙasashen yankin Asiya su suka maye gurbin Turai a matsayin babbar abokiyar kasuwancin Ghana wajen fitar da kayayyaki da kuma shigo da su, a cewar rahoton Hukumar Kididdiga ta Ƙasar. Wani rahoto da Hukumar Ƙiɗiɗɗiga ta Ghana ta fitar, ya nuna jimlar ribar kasuwanci a watanni huɗun farko na shekarar 2024 da ƙasar ta samu ya kai Cedi biliyan 107.6, wanda ya kai ƙwatanƙwacin dalar Amurka biliyan 8.8. Adadin kudin ya ƙunshi Cedi bilIyan 59.5 da aka samu daga kasuwancin kayayyakin da aka fitar zuwa ƙasashen waje da kuma Cedi biliyan 48.1 na kayayyakin da aka shigo da su ƙasar ta Ghana. Rahoton wanda masanin kididdigar gwamnati Farfesa Samuel Annim ya gabatar a babban birnin ƙasar Accra, na ƙunshe cikin bayanan jaridar kasuwanci na watanni huɗun farko (Janairu zuwa Maris) na shekara 2024 da aka fitar. Kazalika bayanan rahoton sun nuna cewa ƙasashen Asiya su suka maye gurbin Turai a matsayin babbar abokiyar cinikayyar Ghana wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashen ƙetare, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na ƙasar (GNA) ya rawaito. Jaridar ta kuma gabatar da ƙiɗiɗɗigar kasuwanci ta ƙasa da ƙasa, inda ta mai da hankali kan watanni huɗun farko na 2024. Alƙaluman sun auna sauye-sauyen da aka samu a tsawon lokaci a farashi da kuma ingancin kayayyakin da ake fita da kuma shigowa da su ƙasar. Rahoton ya kuma bayyana rarar ribar da aka samu a watanni hudun farko na 2024 inda ya kai ƙudin Cedi biliyan 11.5, adadin da ya ninka ribar Cedi biliyan 4.5 sau biyu da aka samu a watannin farko na shekarar 2023. Masanin kididdigar ya ce adadin ya nuna cewa ribar kasuwancin da ƙasar ta samu ya biyo bayan hauhawar farashin kayayyaki maimakon karuwarsu da ake samu. Kazalika Farfesa Annim ya ce rahoton ya kuma tattaro bayanai kan mafi ƙarancin ribar da aka samu wajen fitar da koko zuwa kasashen waje tun daga shekarar 2021. Ribar fitar da kayayyakin kokon a watanni hudun farko na 2024 da aka samu ya ragu zuwa dalar Amurka miliyan 592.2 idan aka ƙwatanta da matsakaicin kuɗin da aka samu na dala 825.8 a watanni huɗun farko na shakarun 2021 da 2022 da kuma 2023.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Jimlar ribar kasuwancin Ghana a wata hudun farko na 2024 ya kai Cedi biliyan 107.6 — Rahoto
Ƙasashen yankin Asiya su suka maye gurbin Turai a matsayin babbar abokiyar kasuwancin Ghana wajen fitar da kayayyaki da kuma shigo da su, a cewar rahoton Hukumar Kididdiga ta Ƙasar. Wani rahoto da Hukumar Ƙiɗiɗɗiga ta Ghana ta fitar, ya nuna jimlar ribar kasuwanci a watanni huɗun farko na shekara...

At a glance
Ƙasashen yankin Asiya su suka maye gurbin Turai a matsayin babbar abokiyar kasuwancin Ghana wajen fitar da kayayyaki da kuma shigo da su, a cewar rahoton Hukumar Kididdiga ta Ƙasar. Wani rahoto da Hukumar Ƙiɗiɗɗiga ta Ghana ta fitar, ya nuna jimlar ribar kasuwanci a watanni huɗun farko na shekara...
