Yilmaz Oner, wanda ya bayar da umarnin kai hare-hare 18 na ta'addanci da suka yi sanadin mutuwar jami'an tsaro 27 da fararen-hula hudu, ya gamu da ajalinsa ne a lardin Agri na ƙasar Turkiyya. Jami'an tsaron Turkiyya sun kawar da 'yan ta'adda biyar a gabashin ƙasar, ciki har da wanda aka daɗe ana nema ruwa-a-jallo. "An kawar da 'yan ta'adda biyar a yankin karkara na gundumar Dogubayazit da ke lardin Agri da kuma ƙauyen Palamut na gundumar Hasankeyf da ke lardin Batman, a wani samame da aka yi wa laƙabi 'BOZDOGAN-43'," in ji Ministan Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida Ali Yerlikaya a saƙon da ya wallafa a shafin X ranar Alhamis. A cikin 'yan ta'addan da aka kawar har da Yilmaz Oner, wanda ke da inkiya Sehmus Malazgirt, wanda kuma kuma ke cikin waɗanda Ma'aikatar take nema ruwa-a-jallo. A cewar Yerlikaya, Oner yana da hannu a hare-hare 18 na ta'addanci da suka yi sanadin mutuwar jami'an tsaro 27 da fararen-hula huɗu, da jikkata jami'an tsaro 68 da fararen-hula biyu. Bayanan sirri sun tabbatar da cewa Oner ne ya bayar da umarni da kai waɗannan hare-hare, in ji ministan. Uku daga cikin 'yan ta'addan da aka halaka suna cikin waɗanda ake neman amma ba ruwa-a-jallo ba. A kusan shekaru 40 da ƙungiyar ta'addanci ta PKK ta kwashe tana kai hare-hare, ta kashe mutum fiye da 40,000, ciki har da mata da yara da jarirai. Ƙasashen Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai sun ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta'addanci.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Jami'an tsaron Turkiyya sun kawar da wani ɗan ta'adda da ake nema ruwa-a-jallo
Yilmaz Oner, wanda ya bayar da umarnin kai hare-hare 18 na ta'addanci da suka yi sanadin mutuwar jami'an tsaro 27 da fararen-hula hudu, ya gamu da ajalinsa ne a lardin Agri na ƙasar Turkiyya. Jami'an tsaron Turkiyya sun kawar da 'yan ta'adda biyar a gabashin ƙasar, ciki har da wanda aka daɗe ana...

لمحة سريعة
Yilmaz Oner, wanda ya bayar da umarnin kai hare-hare 18 na ta'addanci da suka yi sanadin mutuwar jami'an tsaro 27 da fararen-hula hudu, ya gamu da ajalinsa ne a lardin Agri na ƙasar Turkiyya. Jami'an tsaron Turkiyya sun kawar da 'yan ta'adda biyar a gabashin ƙasar, ciki har da wanda aka daɗe ana...
