Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Jami'an tsaron Turkiyya sun 'kassara' 'yan ta'addar PKK/YPG 14 a Arewacin Siriya

Ma'aikatar Tsaro ta ce an kassara 'yan ta'addar da suka kai hari kan sojojin Turkiyya a yankin Tsaron Firat. Jami'an tsaron Turkyya sun kassara 'yan ta'addar PKK/YPG a Arewacin Siriya, in ji Ma'aikatar Tsaro ta Kasar. Sanarwar da Ma'aikatar ta fitar ta ce an kassara 'yan ta'addar da suka buɗe wut...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:12
Jami'an tsaron Turkiyya sun 'kassara' 'yan ta'addar PKK/YPG 14 a Arewacin Siriya
De un vistazo

Ma'aikatar Tsaro ta ce an kassara 'yan ta'addar da suka kai hari kan sojojin Turkiyya a yankin Tsaron Firat. Jami'an tsaron Turkyya sun kassara 'yan ta'addar PKK/YPG a Arewacin Siriya, in ji Ma'aikatar Tsaro ta Kasar. Sanarwar da Ma'aikatar ta fitar ta ce an kassara 'yan ta'addar da suka buɗe wut...

Ma'aikatar Tsaro ta ce an kassara 'yan ta'addar da suka kai hari kan sojojin Turkiyya a yankin Tsaron Firat. Jami'an tsaron Turkyya sun kassara 'yan ta'addar PKK/YPG a Arewacin Siriya, in ji Ma'aikatar Tsaro ta Kasar. Sanarwar da Ma'aikatar ta fitar ta ce an kassara 'yan ta'addar da suka buɗe wuta kan sojojin Turkiyya a yankin Tsaron Firat. Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar 'kassarawa' da nufin kashewa ko kamawa ko miƙa wuyan ƴan ta'addar da ake magana a kai. Turkiyya ta tsaurara ayyukanta na murƙushe ƙungiyoyin ta'addanci a Arewacin Siriya da Iraƙi, bayan wasu sabbin hare-hare da PKK suka kai a ƴan kwanakin nan, inda suka kashe sojojin Turkiyya 21. 'Yan ta'addar PKK na yawan ɓuya a Arewacin Iraƙi da Siriya tare da shirya kai hare-hare cikin iyakokin Turkiyya. A hare-haren ta'addanci da ta dauki shekara 35 tana kaiwa a Turkiyya, kungiyar PKK da Turkiyya da Amurka da Ingila da Tarayyar Turai suka bayyana a matsayin ta ta'addanci, ta yi ajalin sama da mutum 40,000 da suka haɗa da mata da yara ƙanana da jarirai.