Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Jami’an tsaro sun kwance bam a hanyar Zamfara

An dasa bam ɗin ne a hanyar Danjibga zuwa Kuncin Kalgo a Tsafe Jami’an tsaron Nijeriya sun samu nasarar kwance wani bam da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka dasa a kan hanyar Danjibga zuwa Kuncin Kalgo a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara. TRT Hausa Aikin kwance bam ɗin ya gudana ne ta haɗin gw...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:12
Jami’an tsaro sun kwance bam a hanyar Zamfara
Em resumo

An dasa bam ɗin ne a hanyar Danjibga zuwa Kuncin Kalgo a Tsafe Jami’an tsaron Nijeriya sun samu nasarar kwance wani bam da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka dasa a kan hanyar Danjibga zuwa Kuncin Kalgo a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara. TRT Hausa Aikin kwance bam ɗin ya gudana ne ta haɗin gw...

An dasa bam ɗin ne a hanyar Danjibga zuwa Kuncin Kalgo a Tsafe Jami’an tsaron Nijeriya sun samu nasarar kwance wani bam da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka dasa a kan hanyar Danjibga zuwa Kuncin Kalgo a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara. TRT Hausa Aikin kwance bam ɗin ya gudana ne ta haɗin gwiwar rundunar kwance bama-bamai ta ‘yansandan Nijeriya, Sashen Yaƙi da Garkuwa da Mutane, da rundunar EOD ta Sojoji, tare da cikakken tsaro daga rundunar ‘yansandan jihar. TRT Hausa Kakakin rundunar ‘yansandan Zamfara, Yazid Abubakar, ya ce SP Abdulrazak Musa Hassan ne ya jagoranci aikin, inda jami’an suka yi amfani da dabarun ƙwarewa wajen kwance sassan bam ɗin da aka adana domin binciken kimiyya. TRT Hausa Bayan cikakken bincike a yankin, hukumomin tsaro sun ayyana hanyar a matsayin mai aminci, lamarin da ya dawo da kwanciyar hankali ga masu ababen hawa da mazauna yankin. TRT Hausa Hukumomin sun buƙaci al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa, yayin da ake ci gaba da fuskantar barazanar hare-haren ‘yanbindiga a jihohin arewa maso yammacin Nijeriya. TRT Hausa