Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Jami'an tsaron Nijeriya sun kama wasu shugabannin manhajar Binance

Rahotanni sun ce jami'an tsaron Nijeriya sun kama biyu daga cikin manyan shugabannin manhajar hada-hadar kuɗin kirifto ta Binance a wani samame da suka kai musu. Jami'an tsaron Nijeriya sun kama biyu daga cikin shugabannin manhajar hada-hadar kuɗin kirifto wato Binance a wani samame da suka kai m...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:12
Jami'an tsaron Nijeriya sun kama wasu shugabannin manhajar Binance
At a glance

Rahotanni sun ce jami'an tsaron Nijeriya sun kama biyu daga cikin manyan shugabannin manhajar hada-hadar kuɗin kirifto ta Binance a wani samame da suka kai musu. Jami'an tsaron Nijeriya sun kama biyu daga cikin shugabannin manhajar hada-hadar kuɗin kirifto wato Binance a wani samame da suka kai m...

Rahotanni sun ce jami'an tsaron Nijeriya sun kama biyu daga cikin manyan shugabannin manhajar hada-hadar kuɗin kirifto ta Binance a wani samame da suka kai musu. Jami'an tsaron Nijeriya sun kama biyu daga cikin shugabannin manhajar hada-hadar kuɗin kirifto wato Binance a wani samame da suka kai musu, a cewar jaridar the Financial Times, wadda ta ambato wasu majiyoyi da ke da masaniya game da batun ranar Laraba. Shugabannin Binance ɗin sun je Nijeriya ne sakamakon matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na rufe manhajar a ƙasar a makon jiya, sai dai nan-take ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro ya bayar da umarnin tsare su, in ji rahotanni. Masu manjahar ta Binance ba su ce komai ba game da kama shugabannin nasu, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters. Binance: An fara rufe manhajojin Crypto a Nijeriya bisa umarnin gwamnati A makon jiya gwamnatin Nijeriya ta zargi Binance da taka muhimmiyar rawa wajen tashin farashin dala a ƙasar da kuma lalacewar darajar naira abin da ya jefa tattalin arzikin ƙasar cikin mawuyacin hali. Masu musayar kudade da hukumomin Nijeriya na zargin ‘yan crypto musamman masu amfani da Binance da Coinbase da sauran su, da ba da gudunmawa wajen tashin farashin dala Da yake hankalin jama’a ya fi kai wa kan Binance a wannan badakala, mun yi nazari kan mece ce ita. pic.twitter.com/ST5tbrZaRw — TRT Afrika Hausa (@trtafrikaHA) February 22, 2024 Wata majiya daga Hukumar Kula da Sadarwa ta Nijeriya NCC ta tabbatarwa TRT Afrika Hausa cewa an bai wa kamfanoni na waya umarnin ɗaukar matakin, kuma har ma an fara aiki da shi, musamman ga masu amfani da waya. Ranar Talatar da ta wuce, gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, Olayemi Cardoso, ya ce wasu mutane da ba su sani ba "sun yi hada-hadar dala biliyan 26 ta manhajar Binance a Nijeriya a cikin shekara ɗaya da ta wuce". Ya ƙara da cewa hakan yana barazana ga tattalin arziki da tsaron Nijeriya.