Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Jami'an leken asirin Turkiyya sun 'kassara' babban dan ta'addan PKK/YPG a Siriya

Bayan MIT ta gano maboyar dan ta'addar mai suna Mutlu Kacar da ake wa lakabi da Karker Andok a arewacin Siriya ne aka kai farmaki tare da kassara shi. Hukumar leken asiri ta Turkiyya ta 'kassara' jagoran 'yan ta'addar PKK/YPG a garin Aynul Arab na arewacin Siriya, in ji majiyoyin tsaro. A farmaki...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:12
Jami'an leken asirin Turkiyya sun 'kassara' babban dan ta'addan PKK/YPG a Siriya
De un vistazo

Bayan MIT ta gano maboyar dan ta'addar mai suna Mutlu Kacar da ake wa lakabi da Karker Andok a arewacin Siriya ne aka kai farmaki tare da kassara shi. Hukumar leken asiri ta Turkiyya ta 'kassara' jagoran 'yan ta'addar PKK/YPG a garin Aynul Arab na arewacin Siriya, in ji majiyoyin tsaro. A farmaki...

Bayan MIT ta gano maboyar dan ta'addar mai suna Mutlu Kacar da ake wa lakabi da Karker Andok a arewacin Siriya ne aka kai farmaki tare da kassara shi. Hukumar leken asiri ta Turkiyya ta 'kassara' jagoran 'yan ta'addar PKK/YPG a garin Aynul Arab na arewacin Siriya, in ji majiyoyin tsaro. A farmakin da aka kai a wajen iyakar Turkiyya, Hukumar Leken Asiri (MIT) ta 'kassara' Mutlu Kazar, da ake wa lakabi da Karker Andok, wanda shi ne babban jagoran kungiyar ta ta'addncia a gundumar Aynul Arab, in ji majiyar a ranar Litinin. Jami'an tsaron Turkiyya na amfani da kalmar 'kassarawa' da nufin an kashe ko kama dan ta'adda, ko kuma ya miƙa wuya. Kacar da ya shiga kungiyar ta'addancin a 1997, kuma yake da hannu a hare-haren ta'addanci da dama a yankin haftanin na arewacin Iraki a 2009, ya samu raunuka a hannu a idonsa yayin arangama da jami'an tsaro. Kasancewar ayyana shugabancin Sansanin Makhmur Rustem Cudi da ke arewacin Iraki a 2013, yankin Tel Rifat na Siriya a 2015 da kuma shugabancin mayakan PKK/YPG a Tel Rifat a 2020, ya sanya Kacar a farkon wannan shekarar ya zama babban jagoran ƙungiyar a Aynul Arab. A 2022, ya je Al-Malikiyah da ke arewacin Siriya. Shekara guda kafin hakan, ya bayar da umarnin kai hari kan jerin gwanon motocin jami'an tsaron Turkiyya da ke kai Farmakan Firat a arewacin Siriya, wanda hakan ya yi ajalin sojoji a ranar 24 ga Yuli, 2021. Tun shekarar 2016, Ankara ta ƙaddamar da farmakan yaƙi da ta'addanci cikin nasara a iyakokinta da arewacin Siriya, da manufar hana kafa matattarar 'yan ta'adda a yankin, da kuma bayar da damar samar yankunan zaman lafiya ga jama'a. Bayan MIT ta gano maboyar ɗan ta'addan mai suna Mutlu Kacar da ake wa laƙabi da Karker Andok a arewacin Siriya ne aka kai farmaki tare da kassara shi. A hare-hare ta'addanci da take kai wa Turkiyya a cikin shekaru 35, ƙungiyar PKK ta shiga jerin sunayen ƙungiyoyin ta'adda a Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai -- wadda ke da alhakin mutuwar sama da mutum 40,000, da suka hada da mata da yara ƙanana da jarirai. Ƙungiyar YPG ita ce reshen PKK a Siriya.