Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 282 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 38,584 — galibinsu mata da yar –– sannan ya jikkata mutum sama da 88,881, kana mutum fiye da 10,000 na danne a ɓaraguzai. 1351 GMT — Jami’an kare farar hula a Gaza sun zaƙulo gawawwaki 21 na Falasɗinawa daga cikin ɓarguzai a ranar Lahadi bayan wani hari da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza. Wata majiya daga bangaren kiwon lafiya ta bayyana cewa an gano gawar mutum shida sakamakon harin da Isra’ila ta kai a birnin Rafah inda aka kai su asibitin Khan Younis. Haka kuma an ƙara zaƙulo wasu gawawwakin uku daga cikin ɓaraguzai a yammacin Gaza, kamar yadda Hukumar Kare Fararen Hula ta Gaza ta bayyana a wata sanarwa. Jami’an sun ƙara gano wasu gawawwakin goma a unguwar Tel al-Hawa da ke kudu maso yammacin Gaza. Sai kuma mazauna sansanin gudun hijira na Nuseirat sun gano gawawwakin mutum biyu a tsakiyar Zirin Gaza, kamar yadda shaidu suka bayyana. 1026 GMT — Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce akalla mutane 38,584 ne suka mutu a yakin da Isra'ila ta yi kan yankin da aka yi wa kawanya. Adadin wadanda suka mutun ya ƙunshi mutuwar mutum 141 a cikin sa'o'i 24, in ji sanarwar ma'aikatar, ta kuma kara da cewa mutum 88,881 ne suka jikkata a Gaza tun bayan fara yakin.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Jami'ai a Gaza sun zaƙulo gawawwakin Falasɗinawa 21 daga cikin ɓaraguzai
Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 282 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 38,584 — galibinsu mata da yar –– sannan ya jikkata mutum sama da 88,881, kana mutum fiye da 10,000 na danne a ɓaraguzai. 1351 GMT — Jami’an kare farar hula a Gaza sun zaƙulo gawawwaki 21 na Falasɗinawa daga cikin ɓa...

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 282 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 38,584 — galibinsu mata da yar –– sannan ya jikkata mutum sama da 88,881, kana mutum fiye da 10,000 na danne a ɓaraguzai. 1351 GMT — Jami’an kare farar hula a Gaza sun zaƙulo gawawwaki 21 na Falasɗinawa daga cikin ɓa...
