Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Jamhuriyyar Kongo da 'yan tawayen M23 sun cim ma yarjejeniya domin dakatar da rikici a gabashin DRC

An cim ma yarjejeniyar ne bayan ɓangarorin biyu sun shafe watanni uku suna tattaunawa a Doha babban birnin Qatar. Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da ƙungiyar 'yan tawayen M23 da ake zargin tana samun goyon bayan Rwanda, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar Asabar, domin...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:12
Jamhuriyyar Kongo da 'yan tawayen M23 sun cim ma yarjejeniya domin dakatar da rikici a gabashin DRC
At a glance

An cim ma yarjejeniyar ne bayan ɓangarorin biyu sun shafe watanni uku suna tattaunawa a Doha babban birnin Qatar. Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da ƙungiyar 'yan tawayen M23 da ake zargin tana samun goyon bayan Rwanda, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar Asabar, domin...

An cim ma yarjejeniyar ne bayan ɓangarorin biyu sun shafe watanni uku suna tattaunawa a Doha babban birnin Qatar. Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da ƙungiyar 'yan tawayen M23 da ake zargin tana samun goyon bayan Rwanda, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar Asabar, domin kawo ƙarshen rikicin da ya addabi gabashin ƙasar mai arzikin ma’adanai amma cike da rikice-rikice. An cim ma yarjejeniyar ne bayan ɓangarorin biyu sun shafe watanni uku suna tattaunawa a Doha babban birnin Qatar. Wannan na zuwa ne bayan wata yarjejeniya ta daban da aka cim ma tsakanin Congo da Rwanda a birnin Washington a watan da ya gabata. Kungiyar M23, wadda ta mamaye manyan yankuna a gabashin DRC cikin wata guda a watan Janairu da Fabrairu, inda ta dage kan cewa tana son ƙulla yarjejeniya ta musamman da gwamnatin Kinshasa, saboda yarjejeniyar Washington ta bar wasu "muhimman matsaloli" a gefe. Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yaba da wannan ci gaba, tana mai cewa: "Wannan muhimmin ci gaba ne da ke nuna sahihancin ƙoƙarin kawo zaman lafiya da dawwamammen tsaro a gabashin DRC da kuma yankin Great Lakes A cewar yarjejeniyar, bangarorin sun kuma amince da fara tattaunawa don ƙulla cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya, tare da samar da taswirar dawo da ikon gwamnati a yankunan gabashin DRC da ke ƙarƙashin ikon ‘yan tawaye.