Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Jamhuriyar Benin ta hana Nijar fitar da fetur saboda rikicin kan iyaka

Nijar ta rufe iyakokinta daga shigar da kayayyaki daga Benin, kuma ba ta faɗa wa Benin dalilin yin hakan a hukumance ba, in ji Talon a cikin wata sanarwa. Jamhuriyyar Benin ta hana fitar da man fetur daga Nijar ta tashar jiragen ruwa, in ji shugaban ƙasar Patrice Talon a ranar jiya Laraba, inda y...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:12
Jamhuriyar Benin ta hana Nijar fitar da fetur saboda rikicin kan iyaka
En bref

Nijar ta rufe iyakokinta daga shigar da kayayyaki daga Benin, kuma ba ta faɗa wa Benin dalilin yin hakan a hukumance ba, in ji Talon a cikin wata sanarwa. Jamhuriyyar Benin ta hana fitar da man fetur daga Nijar ta tashar jiragen ruwa, in ji shugaban ƙasar Patrice Talon a ranar jiya Laraba, inda y...

Nijar ta rufe iyakokinta daga shigar da kayayyaki daga Benin, kuma ba ta faɗa wa Benin dalilin yin hakan a hukumance ba, in ji Talon a cikin wata sanarwa. Jamhuriyyar Benin ta hana fitar da man fetur daga Nijar ta tashar jiragen ruwa, in ji shugaban ƙasar Patrice Talon a ranar jiya Laraba, inda ya buƙaci Nijar ta sake buɗe kan iyakarta don shigar da kayayyakin Benin tare da daidaita hulɗa tsakaninsu kafin a fara jigilar ɗanyen mai. Matakin ya kawo cikas ga shirin Nijar na fara fitar da kayayyaki daga rijiyar manta ta Agadem a watan jiya tare da babban kamfanin mai na China National Petroleum Corp (CNPC) na dalar Amurka miliyan 400. An yi hasashen za a daidaita harkokin kasuwanci a yankin bayan da ƙungiyar Ƙasashen Yammacin Afirka ta ɗage takunkumin da ta ƙaƙaba wa Nijar a watan Fabrairun da ya gabata, yayin da take ƙoƙarin hana ta ita da maƙwabtanta Mali da Burkina Faso da ke ƙarƙashin mulkin soja ficewa daga ƙungiyar ta siyasa da tattalin arziki. Sai dai Nijar ta rufe iyakokinta daga shigar da kayayyaki daga Benin, kuma ba ta faɗa wa Benin dalilin yin hakan a hukumance ba, in ji Talon a cikin wata sanarwa. "Idan kuna so ku loda manku ... a cikin ruwanmu, to bai kamata ku kalli Benin a matsayin abokiyar gaba ba," in ji shi. "Idan gobe hukumomin Nijar suka yanke shawarar yin hadin gwiwa da ƙasar Benin, to za a yi lodin mai a jiragen ruwa."