Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Benin da AU sun yi Allah wadai da harin ta’addanci a Nijeriya

Harin a jihar Kwara ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 170 Jamhuriyar Benin da Tarayyar Afirka (AU) sun bayyana ta’aziyyarsu tare da yin Allah wadai da wani harin ta’addanci da aka kai a Nijeriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 170, kamar yadda aka bayyana a ranar Alhamis. TRT Hau...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:12
Benin da AU sun yi Allah wadai da harin ta’addanci a Nijeriya
De un vistazo

Harin a jihar Kwara ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 170 Jamhuriyar Benin da Tarayyar Afirka (AU) sun bayyana ta’aziyyarsu tare da yin Allah wadai da wani harin ta’addanci da aka kai a Nijeriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 170, kamar yadda aka bayyana a ranar Alhamis. TRT Hau...

Harin a jihar Kwara ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 170 Jamhuriyar Benin da Tarayyar Afirka (AU) sun bayyana ta’aziyyarsu tare da yin Allah wadai da wani harin ta’addanci da aka kai a Nijeriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 170, kamar yadda aka bayyana a ranar Alhamis. TRT Hausa Gwamnatin Benin ta miƙa “ta’aziyya ta musamman” ga iyalan waɗanda abin ya shafa, al’ummar Nijeriya da gwamnati, tare da sake jaddada goyon bayanta ga ƙoƙarin Abuja na yaƙi da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi a yankin. TRT Hausa Shugaban Hukumar AU, Mahmoud Ali Youssouf, ya bayyana harin a matsayin mummunan aiki da rashin imani, yana mai cewa babban take haƙƙin ɗan’adam ne kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro, kamar yadda sanarwar AU ta bayyana. TRT Hausa Youssouf ya miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu tare da tabbatar da cikakken goyon bayan AU ga gwamnatin Nijeriya da hukumomin Jihar Kwara. TRT Hausa Gwamnatin Jihar Kwara ta ce an riga an binne mutum 75 a kabarin bai-ɗaya, yayin da wani ɗan majalisa ya bayyana cewa an gano gawawwaki 170, kuma ana sa ran adadin zai ƙaru yayin da ake ci gaba da bincike. TRT Hausa Jihar Kwara dai na fuskantar ƙarin matsalolin tsaro a ‘yan watannin nan, musamman a yankunan da ke kusa da dazuzzuka, sakamakon hare-haren ‘yan fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma matsin lambar soji a jihohin maƙwabta. TRT Hausa