Kuri'ar jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan na nuna raguwar farin jinin jam'iyyar Likud ta Netanyahu tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da yakinta kan Gaza. Yayin da kasashen duniya ke ci gaba da yi wa Isra'ila raddi kan take hakkin bil'adama tare da bayyana kisan gillar da ake yi wa Falasdinawa a matsayin "kisan kare dangi," ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya-bayan nan ta nuna cewa Jam'iyyar Likud ta masu tsaurin ra'ayi ta Firaiminista Benjamin Netanyahu za ta rasa rabin 'yan majalisarta a majalisar dokokin kasar idan da za a gudanar da zabe a yanzu. Bisa ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da tashar Isra'ila ta Channel 13 ta fitar da yammacin jiya Alhamis, Jam'iyyar Likud za ta lashe kujeru 16 ne kawai a majalisar dokokin kasar idan da za a gudanar da zabe a yau. A halin yanzu, Likud na da kujeru 32 a cikin mambobi 120 na Majalisar Dokokin ta Knesset. Binciken ya nuna cewa jam'iyyar Unity National, mai sassaucin ra'ayi kuma ta ƙawancen siyasa karkashin jagorancin tsohon ministan tsaro Benny Gantz, za ta zamo ita ce jam'iyya mafi girma a majalisar dokokin Knesset mai kujeru 38, sama da kujeru 12 da take da su yanzu. Ita ma jam'iyyar Yesh Atid (There is a Future) da Yair Lapid ke jagoranta ta yi asarar farin jininta, kamar yadda binciken ya nuna, kuma za ta rasa ƙarfinta na majalisar daga 'yan majalisa 24 zuwa 15 kuma za ta kasance jam'iyya ta uku mafi girma a majalisar dokokin kasar idan an gudanar da zabe a yanzu. Kuri'u na baya-bayan nan sun nuna koma baya ga farin jinin Likud a 'yan watannin da suka gabata. Tashar Channel 13 ta Isra'ila ta yi sharhi tana cewa "Likud na ci gaba da rushewa tun bayan ɓarkewar yaƙin, idan aka gudanar da zabe a yau, jam'iyyar Firaiminista Benjamin Netanyahu za ta lashe kujeru 16 kacal, wanda ya zarce jam'iyyar Yair Lapid." Support eroding Tashar ta yi nuni da cewa, idan har aka gudanar da zabuka a yanzu, Likud da jam'iyyun ƙawancen da suka hada da Shas masu tsattsauran ra'ayi da kuma United Torah Judaism, da jam'iyyun masu ra'ayin mazan jiya na Yahudawa, za su samu kujeru 45 kawai idan aka kwatanta da wanda suke da su 64 a yanzu. Kafa gwamnati a Isra'ila na buƙatar amincewar aƙalla mambobi 61 na majalisar dokokin Knesset. Saɓanin ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuni da cewa jam'iyyun adawa za su iya lashe kujeru 71, yayin da jam'iyyar Democratic Front for Peace (Hadash) da kuma ƙawancen Arab Movement for Change (Taal) suka samu kujeru hudu. Binciken ya kuma nuna cewa idan aka musanya Netanyahu a matsayin jagiran jam'iyyar Likud da tsohon shugaban hukumar leƙen asirin ƙsar ta Mossad, Yossi Cohen, jam'iyyar za ta samu kujeru 23, idan aka kwatanta da jam'iyyar National Unity. Tashar talabijin din ta ce wani ƙwararre kan sha'anin zaɓe a Isra'ila Camil Fuchs ne ya aiwatar da ƙuri'ar jin ra'ayin, inda ya haɗo ra'ayin Isra'ilawa 700. Kawo yanzu dai babu wata alama da ke nuna yiwuwar gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a daidai lokacin da ake ci gaba da yakin Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba. Sai dai alkaluman da Isra'ila ta yi na nuni da yiwuwar sake komawa rumfunan zabe bayan yakin.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Jam'iyyar Likud ta Netanyahu za ta rasa rabin kujerun majalisar dokoki - Kuri'ar ra'ayin jama'a
Kuri'ar jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan na nuna raguwar farin jinin jam'iyyar Likud ta Netanyahu tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da yakinta kan Gaza. Yayin da kasashen duniya ke ci gaba da yi wa Isra'ila raddi kan take hakkin bil'adama tare da bayyana kisan gillar da ake yi wa Falasdinawa...

A taƙaice
Kuri'ar jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan na nuna raguwar farin jinin jam'iyyar Likud ta Netanyahu tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da yakinta kan Gaza. Yayin da kasashen duniya ke ci gaba da yi wa Isra'ila raddi kan take hakkin bil'adama tare da bayyana kisan gillar da ake yi wa Falasdinawa...
