Ana sa ran Shugaba Cyril Ramaphosa da wanda ya gabace shi wanda ba sa ga maciji da juna Jacob Zuma gabatar da jawabi a taruka daban-daban waɗanda za su gudanar a lardin KwaZulu-Natal, wanda muhimmin yanki ne ga zaɓen ƙasar. Jam'iyya mai mulki ta ANC a Afirka ta ta Kudu na ƙaddamar da yaƙin neman zaɓenta a ranar Asabar domin shirin zaɓen ƙasar da za a gudanar a ranar 29 ga watan Mayu, wanda jam'iyyar za ta fuskanci zaɓe mafi ƙalubale a tarihinta sakamakon matsalolin rashin aiki yi da matsalolin tattalin arziƙi da ƙasar ke fuskanta. Ana sa ran Shugaba Cyril Ramaphosa da wanda ya gabace shi wanda ba sa ga maciji da juna Jacob Zuma gabatar da jawabi a taruka daban-daban waɗanda za su gudanar a lardin KwaZulu-Natal, wanda muhimmin yanki ne ga zaɓen ƙasar. Jam'iyyar ANC wadda ke kan mulki a ƙasar tun 1994 bayan shigowar dimokuraɗiyyar, a halin yanzu tana fama da ƙarancin goyon baya inda kuma ake yi mata zargin cin hanci da rashawa. Tasirin Zuma Sakamakon ya jima yana jin haushin yadda aka tilasta masa sauka daga kan muƙaminsa na shugaban ƙasa, tsohon shugaban ya shiga wata jam'iyya ta adawa domin ƙoƙarin rage wa ANC ƙuri'u. "Zuma shi ne babbar barazana ga ANC a KwaZulu-Natal," in ji Zakhele Ndlovu, wanda malamin siyasa ne a Jam'iar KwaZulu-Natal da ke Durban. Rikicin da ke tsakanin shugabannin biyu zai fito fili ne a ranar Asabar, lokacin da jam’iyyar ANC ke sa ran magoya baya 85,000 za su cika filin wasan kwallon kafa a birnin Durban domin kaddamar da shirinta na zaben. Yiwuwar haɗaka Lardi na biyu wanda ya fi yin suna a Afirka ta Kudu shi ne KwaZulu-Natal wanda ake kallonsa a matsayin wani zakaran gwajin dafi dangane da nasarar ANC a zaɓe. Lardin ne ke mambobi ƴan ANC mafi yawa sai dai a halin yanzu jam'iyyar na cikin matsi sakamakon haɗaka da aka yi tsakanin Democratic Alliance da ƙawarta nkatha Freedom Party. "Idan ANC ba ta taka rawar a zo a gani a KwaZulu-Natal ba, ba za ta samu nasara a ƙasa ba," in ji Susan Booysen, wanda wani nmai sharhi ne kan siyasa ga cibiyar Mapungubwe Institute for Strategic Reflection.. Ƙuri'ar jin ra'ayi ta nuna cewa jam'iyyar za ta iya samun aƙalla kaso 40 cikin 100 na ƙuri'un ƙasar, wanda hakan zai iya tilasta mata ta buƙaci gwamnatin haɗaka ta ci gaba da mulki. Sai dai sakamakon matsalolu na kasafin kuɗi, ba lallai ne Ramaphosa ya yi manyan alƙawura na zaɓe ba.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Jam'iyyar ANC ta Afirka ta Kudu na ƙaddamar da yaƙin neman zaɓenta
Ana sa ran Shugaba Cyril Ramaphosa da wanda ya gabace shi wanda ba sa ga maciji da juna Jacob Zuma gabatar da jawabi a taruka daban-daban waɗanda za su gudanar a lardin KwaZulu-Natal, wanda muhimmin yanki ne ga zaɓen ƙasar. Jam'iyya mai mulki ta ANC a Afirka ta ta Kudu na ƙaddamar da yaƙin neman...

Ana sa ran Shugaba Cyril Ramaphosa da wanda ya gabace shi wanda ba sa ga maciji da juna Jacob Zuma gabatar da jawabi a taruka daban-daban waɗanda za su gudanar a lardin KwaZulu-Natal, wanda muhimmin yanki ne ga zaɓen ƙasar. Jam'iyya mai mulki ta ANC a Afirka ta ta Kudu na ƙaddamar da yaƙin neman...
