Tsohon zakaran damben boksin ajin babban nauyi Mike Tyson ya soma damben da ƙarfinsa inda ya ƙwace iko da damben a zagaye na farko da na biyu, sai dai daga bisani Paul ya girgije inda ya samu nasara kan Tyson. Fitaccen mai yin bidiyo a YouTube kuma ɗan dambe Jake Paul, ya doke shahararren ɗan damben duniya Mike Tyson a wani muhimmin dambe na ajin babban nauyi. Paul ya doke Tyson ne bayan ra'ayin alƙalai ya zo ɗaya inda suka ayyana shi a matsayin wanda ya ci damben. An gudanar da damben ne a ranar Asabar a filin wasa na Arlington mai ɗaukar mutum 80,000 a Texas. Tsohon zakaran damben boksin ajin babban nauyi Mike Tyson ya soma damben da ƙarfinsa inda ya ƙwace iko da damben a zagaye na farko da na biyu. Sai dai Paul ya girgije inda ya ƙwace iko da damben daga bisani inda ya rinƙa dukan Tyson har ya samu maki a ƙarshen zagaye na takwas. Paul ya sunkuya ga Tyson a zagayen ƙarshen na damben domin nuna girmamawa ga Tyson mai shekara 88. Paul mai shekara 27 a halin yanzu ya fafata a karo na na 12 a dambensa na ajin ƙwararru inda a cikin damben 12 ya samu nasara sau 11. Ya yi rashin nasara a dambensa na bakwai tsakaninsa da Tommy Fury. Daga cikin nasara 11 da ya yi, ya samu nasara bakwai ne ta hanyar yi wa abokan dambensa kwab-ɗaya.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Jake Paul ya doke Mike Tyson a damben boksin
Tsohon zakaran damben boksin ajin babban nauyi Mike Tyson ya soma damben da ƙarfinsa inda ya ƙwace iko da damben a zagaye na farko da na biyu, sai dai daga bisani Paul ya girgije inda ya samu nasara kan Tyson. Fitaccen mai yin bidiyo a YouTube kuma ɗan dambe Jake Paul, ya doke shahararren ɗan dam...

At a glance
Tsohon zakaran damben boksin ajin babban nauyi Mike Tyson ya soma damben da ƙarfinsa inda ya ƙwace iko da damben a zagaye na farko da na biyu, sai dai daga bisani Paul ya girgije inda ya samu nasara kan Tyson. Fitaccen mai yin bidiyo a YouTube kuma ɗan dambe Jake Paul, ya doke shahararren ɗan dam...
