Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Jagoran 'yan-awaren Biafra: Babbar Kotu a Nijeriya ta samu Nnamdi Kanu da laifin ta'addanci

Alƙalin kotun ya ce masu shigar da ƙara sun kawo shaidun da suka nuna cewa Nnamdu Kanu ya tunzura munanan hare-haren kan jami'an tsaro da kuma 'yan Nijeriya da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Wata Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya a ranar Alhamis ta samu shugaban 'yan-aware da ke fafutukar kafa ƙsar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:12
Jagoran 'yan-awaren Biafra: Babbar Kotu a Nijeriya ta samu Nnamdi Kanu da laifin ta'addanci
En bref

Alƙalin kotun ya ce masu shigar da ƙara sun kawo shaidun da suka nuna cewa Nnamdu Kanu ya tunzura munanan hare-haren kan jami'an tsaro da kuma 'yan Nijeriya da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Wata Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya a ranar Alhamis ta samu shugaban 'yan-aware da ke fafutukar kafa ƙsar...

Alƙalin kotun ya ce masu shigar da ƙara sun kawo shaidun da suka nuna cewa Nnamdu Kanu ya tunzura munanan hare-haren kan jami'an tsaro da kuma 'yan Nijeriya da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Wata Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya a ranar Alhamis ta samu shugaban 'yan-aware da ke fafutukar kafa ƙsar Biafra Nnamdi Kanu, da laifukan da suka shafi ta'addanci, a cewar hukuncin da Alkali James Omotosho ya yanke. Omotosho ya ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da cewa maganganun da Kanu ya yi a rediyo da umarnin da ya bayar daga ƙungiyarsa ta Indigenous People of Biafra (IPOB) wadda a yanzu aka haramta ayyukanta, sun haddasa hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaro da fararen-hula a yankin kudu maso gabas a cikin ƙoƙarinsa na neman kafa ƙasar Biafra mai cin gashin kanta. Yunkurin yankin na ɓallewa a matsayin Jamhuriyar Biafra a 1967 ya haifar da yaƙin basasa na shekaru uku wanda ya kashe fiye da miliyan ɗaya. An kama Kanu a karon farko a 2015, amma ya tsere daga Nijeriya yayin da yake a kan beli a 2017. Daga bisani an sake kama shi a Kenya a 2021, sannan aka tuhume shi a Nijeriya da laifukan ta'addanci guda bakwai. Kanu ya musanta waɗannan tuhume-tuhumen.