"Muna gwagwarmaya ne domin ‘yanta ƙasarmu tare da yin fito-na-fito da 'yan mamaya da kuma aniyarsu ta faɗaɗa mamaya a yankin Gabas ta Tsakiya," a cewar jagoran Hezbollah, Naim Qassem. Sabon shugaban Hezbollah ya ce ƙungiyarsa ba ta faɗa a madadin Iran, amma domin kare ƙasar Lebanon da 'yantar da ita. "Mu a Lebanon ba ma yaƙi a madadin Iran ko kuma domin mu aiwatar da shirinta, sai domin kare ƙasarmu da 'yantar da ita," a cewar Naim Qassem a wani jawabi da aka naɗa ranar Laraba. "Mun kwashe watanni 11 muna cewa ba ma son yaƙi, amma a shirye muke idan aka tilasta mana shi." An naɗa Qassem a matsayin sabon shugaban Hezbollah ranar Talata, inda ya gaji Hassan Nasrallah, wanda aka kashe a wani harin sama da Isra’ila ta kai Beirut a watan jiya. "Niyyata ce na ci gaba da salon Nasrallah na kasance a kan hanyar yaƙi bisa ga yadda abubuwa ke wakana," in ji shi. "Gwagwarmayar ta kasance ne domin ‘yanta ƙasarmu da yin fito-na-fito da masu mamaya da kuma niyyarsu ta faɗaɗa mamaya a yankin." Taimaka wa Gaza Shugaban na Hezbollah ya ce taimaka wa Gaza ya zama wajibi domin "ƙalubalantar barazanar da Isra’ila ke yi wa Zirin Gaza, kuma mutanen Gaza suna da ‘yanci a matsayinsu na mutane da Larabawa da Musulmai da kuma na ‘yan ƙasa na dukkanmu mu mara musu baya ". "Wannan yaƙin ba da Isra’ila kawai muke yinsa ba; muna yaƙi da Amurka da Turai da kuma wasu ƙasashen duniya; ya haɗa da duk ababen da ake amfani da su wajen shafe gwagwarmaya da kuma mutanen yankin daga doron ƙasa ta hanyar zalunci da halaka da kuma aikata laifuka." A watan da ya gabata ne Isra’ila ta kai hare-hare masu yawa a Lebanon kan wuraren da ta yi iƙirarin cewa na Hezbollah ne a wani lamari da ya ta'azzara hare-haren wuce-gona-da-iri da aka shefe shekara ɗaya ana yi tsakanin Isra’ila da kuma ƙungiyar tun lokacin da Isra’ila ta fara yaƙinta na rashin tausayi a Gaza. Fiye da mutum 2,700 aka kashe kuma kusan mutum 12,500 suka jikkata sakamakon hare-haren Isra’ila tun watan Oktoban bara, a cewar hukumomin kiwon lafiyar Lebanon. Isra’ila ta faɗaɗa yaƙin ranar ɗaya ga watan Oktoba ta hanyar kai farmaki kudancin Lebanon.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Jagoran Hezbollah: 'Ba ma yaƙi domin Iran, sai don kare ƙasarmu'
"Muna gwagwarmaya ne domin ‘yanta ƙasarmu tare da yin fito-na-fito da 'yan mamaya da kuma aniyarsu ta faɗaɗa mamaya a yankin Gabas ta Tsakiya," a cewar jagoran Hezbollah, Naim Qassem. Sabon shugaban Hezbollah ya ce ƙungiyarsa ba ta faɗa a madadin Iran, amma domin kare ƙasar Lebanon da 'yantar da...

At a glance
"Muna gwagwarmaya ne domin ‘yanta ƙasarmu tare da yin fito-na-fito da 'yan mamaya da kuma aniyarsu ta faɗaɗa mamaya a yankin Gabas ta Tsakiya," a cewar jagoran Hezbollah, Naim Qassem. Sabon shugaban Hezbollah ya ce ƙungiyarsa ba ta faɗa a madadin Iran, amma domin kare ƙasar Lebanon da 'yantar da...
