Kafafen watsa labaran kasar sun ce mutanen sun yi barazanar ce bayan Firaiminista Netanyahu ya ki ganawa da kungiyar kusan iyalai 100 na mutanen da aka yi garkuwa da su. Iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza da aka mamaye sun yi barazanar soma yajin cin abinci har sai gwamnatin Isra'ila mai tsaurin ra'ayi ta kulla yarjejeniyar musayar fursunoni da kungiyar Hamas mai kare hakkin Falasdinawa, a cewar kafofin watsa labaran kasar. Ranar Juma'a jaridar Yedioth Ahronoth ta ce mutanen sun yi barazanar ce bayan Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ki ganawa da iyalans mutanen da aka yi garkuwa da su. Ta ce kusan mutum 100 ne suka zargi Netanyahu da yunkurin raba kawunan kungiyar iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su domin ba ya so ya biya bukatunsu. Yedioth Ahronoth ta ce iyalan mutanen sun bai wa Netanyahu wa'adi zuwa yau Asabar da maraice domin ya gana da su da kuma tabbatar da sakin 'yan uwansu. Mutanen sun ce hare-haren da dakarun Isra'ila suke ci gaba da kaiwa a Gaza sun hana yunkurin sako 'yan uwansu, a cewar jaridar. Gwamnatin Isra'ila mai tsaurin ra'ayi ba ta ce komai game da barazanar da mutanen suka yi ta soma yajin cin abinci ba.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Iyalan Isra'ilawa da aka yi garkuwa da su sun yi barazanar soma yajin cin abinci bayan Netanyahu ya ki saurarensu
Kafafen watsa labaran kasar sun ce mutanen sun yi barazanar ce bayan Firaiminista Netanyahu ya ki ganawa da kungiyar kusan iyalai 100 na mutanen da aka yi garkuwa da su. Iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza da aka mamaye sun yi barazanar soma yajin cin abinci har sai gwamnatin Isra'ila m...

At a glance
Kafafen watsa labaran kasar sun ce mutanen sun yi barazanar ce bayan Firaiminista Netanyahu ya ki ganawa da kungiyar kusan iyalai 100 na mutanen da aka yi garkuwa da su. Iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza da aka mamaye sun yi barazanar soma yajin cin abinci har sai gwamnatin Isra'ila m...
