الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Ivory Coast ta umarci sojojin Faransa su fice daga ƙasar

Shugaban na Ivory Coast ya ce yanzu sojojin ƙasarsa za su maye gurbin na Faransa a Bataliya ta 43 ta Sojojin Ruwa a Port Bouet da ke kudancin Abidjan inda dakarun Faransa suka yi sansani. Sojojin Faransa za su fice daga ƙasar Ivory Coast a watan nan na Janairu, a cewar shugaban ƙasar Alassane Oua...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:12 ص
Ivory Coast ta umarci sojojin Faransa su fice daga ƙasar
لمحة سريعة

Shugaban na Ivory Coast ya ce yanzu sojojin ƙasarsa za su maye gurbin na Faransa a Bataliya ta 43 ta Sojojin Ruwa a Port Bouet da ke kudancin Abidjan inda dakarun Faransa suka yi sansani. Sojojin Faransa za su fice daga ƙasar Ivory Coast a watan nan na Janairu, a cewar shugaban ƙasar Alassane Oua...

Shugaban na Ivory Coast ya ce yanzu sojojin ƙasarsa za su maye gurbin na Faransa a Bataliya ta 43 ta Sojojin Ruwa a Port Bouet da ke kudancin Abidjan inda dakarun Faransa suka yi sansani. Sojojin Faransa za su fice daga ƙasar Ivory Coast a watan nan na Janairu, a cewar shugaban ƙasar Alassane Ouattara a wani jawabi na bikin ƙarshen shekara da ya yi wa 'yan ƙasar ranar Talata. Ouattara ya ce: “Za mu yi alfahari da sojojinmu, waɗanda suke aiki bisa ƙwarewa. Don haka mun yanke shawarar janye dakarun Faransa daga Cote d’Ivoire cikin lumana.” Shugaban na Ivory Coast ya ce yanzu sojojin ƙasarsa za su maye gurbin na Faransa a Bataliya ta 43 ta Sojojin Ruwa a Port Bouet da ke kudancin Abidjan inda dakarun Faransa suka yi sansani. Rukunin karshe na sojojin Faransa na kammala ficewa daga Nijar Ivory Coast ta bi sahun ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, waɗanda suka kori dakarun Faransa daga cikinsu bayan sun zarge su da hannu wajen tayar da rikice-rikice. Hakan na nuna yadda ƙasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka suke ci gaba da yi mata bore, lamarin da ya rage tasirinta a nahiyar Afirka.