Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Istanbul zai karɓi baƙuncin gasar UEFA Europa ta 2026, da gasar Conference ta 2027

Kwamitin zartarwa na hukumar UEFA ya yanke cewa za a gudanar da wasannin ƙarshe na gasar Europa ta 2026 da na Conference na 2027 a filin wasa na Besiktas da ke birnin Istanbul. Hukumar gudanarwa ƙwallon ƙafa a Turai, ya yanke cewa za a gudanar da wasan ƙarshe na gasar Europa na 2026 a filin wasa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:12
Istanbul zai karɓi baƙuncin gasar UEFA Europa ta 2026, da gasar Conference ta 2027
A taƙaice

Kwamitin zartarwa na hukumar UEFA ya yanke cewa za a gudanar da wasannin ƙarshe na gasar Europa ta 2026 da na Conference na 2027 a filin wasa na Besiktas da ke birnin Istanbul. Hukumar gudanarwa ƙwallon ƙafa a Turai, ya yanke cewa za a gudanar da wasan ƙarshe na gasar Europa na 2026 a filin wasa...

Kwamitin zartarwa na hukumar UEFA ya yanke cewa za a gudanar da wasannin ƙarshe na gasar Europa ta 2026 da na Conference na 2027 a filin wasa na Besiktas da ke birnin Istanbul. Hukumar gudanarwa ƙwallon ƙafa a Turai, ya yanke cewa za a gudanar da wasan ƙarshe na gasar Europa na 2026 a filin wasa na ƙungiyar Besiktas, wato filin Tupras Stadium da ke Istanbul. Haka nan kuma, birnin na Istanbul zai karɓi baƙuncin wasan ƙarshe na gasar Europa Conference ta 2027. A sanarwar da mamban kwamitin gudanarwa na UEFA, Servet Yardimci ya fitar, taron na hukumar UEFA ya gudana ne a birnin Dublin babban birnin Ireland, a Laraba. Filin wasa na Tupras Stadium, wanda a baya ake kira da Vodafone Park, shi ne ya karɓi baƙuncin gasar UEFA Super Cup ta 2019, inda aka buga wasa tsakanin Liverpool da Chelsea.