A cewar Hukumar Falasɗinawa mai Kula da Walwalar Waɗanda aka Tsare, yanzu, haka akwai Falasɗinawa 10,400 a gidajen yarin Isra’ila, da suka haɗa da mutanen da aka kama a Gaza lokacin yaƙin da Isra’ila ta shafe watanni 15 tana yi a Gaza. Ma’aikatar shari’a ta Isra’ila ta saki sunayen Falasɗinawa 95 da za a saki ranar Lahadi sakamakon aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza. Sunayen sun ƙunshi na mata da matasa da suka kai har shekara 25. Daga cikin matan da za a saki akwai Dalal al Arouri, ‘yar’uwar Saleh al Arouri, mataimakin shugaban Hamas wanda Isra’ila ta kashe a watan Janairun bara. Sunayen sun kuma ƙunshi na wata ‘yar jarida Bushra al Taweel, wacce aka saki a musayar fursunoni da aka yi a baya a 2011 tsakanin Hamas da Isra’ila. ‘Ya ce ga wani babban jagoran Hamas Jamal al Taweel wanda ya taɓa zama magajin garin birnin Al Bireh da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye. Khalid Jarrar, fitaccen jagoran wata ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa mai ra’yin gurguzu PLFP kuma wakili a Majalisar Dokoin Falasɗinawa, shi ma yana cikin waɗanda za a saki. A yanzu haka akwai Falasɗinawa 10,400 a gidajen yarin Isra’ila, da suka haɗa da mutanen da aka kama a Gaza lokacin yaƙin da Isra’ila ta shafe watanni 15 tana yi a Gaza, kamar yadda Hukumar Falasɗinawa mai Kula da Walwalar Waɗanda aka Tsare da Kuma Ƙungiyar Fursunoni ta Falasaɗinawa su faɗa.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Isra'ila za ta saki Falasɗinawa 95 a ranar farko ta tsagaita wuta a Gaza
A cewar Hukumar Falasɗinawa mai Kula da Walwalar Waɗanda aka Tsare, yanzu, haka akwai Falasɗinawa 10,400 a gidajen yarin Isra’ila, da suka haɗa da mutanen da aka kama a Gaza lokacin yaƙin da Isra’ila ta shafe watanni 15 tana yi a Gaza. Ma’aikatar shari’a ta Isra’ila ta saki sunayen Falasɗinawa 95...

At a glance
A cewar Hukumar Falasɗinawa mai Kula da Walwalar Waɗanda aka Tsare, yanzu, haka akwai Falasɗinawa 10,400 a gidajen yarin Isra’ila, da suka haɗa da mutanen da aka kama a Gaza lokacin yaƙin da Isra’ila ta shafe watanni 15 tana yi a Gaza. Ma’aikatar shari’a ta Isra’ila ta saki sunayen Falasɗinawa 95...
