الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Isra'ila za ta ɗanɗana kuɗarta kan gallazawar da take yi wa al'ummar Gaza — Erdogan

"Ko mene ne zai faru, mu (Turkiyya) za mu ci gaba da tunkarar Isra'ila kan rashin imanin da take yi a Gaza, kuma tabbas za ta ɗanɗana kuɗarta kan laifukan da ta aikata," kamar yadda daraktan sadarwa na ƙasar ya ambato Shugaba Erdogan yana f Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi magana ta w...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:12 ص
Isra'ila za ta ɗanɗana kuɗarta kan gallazawar da take yi wa al'ummar Gaza — Erdogan
لمحة سريعة

"Ko mene ne zai faru, mu (Turkiyya) za mu ci gaba da tunkarar Isra'ila kan rashin imanin da take yi a Gaza, kuma tabbas za ta ɗanɗana kuɗarta kan laifukan da ta aikata," kamar yadda daraktan sadarwa na ƙasar ya ambato Shugaba Erdogan yana f Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi magana ta w...

"Ko mene ne zai faru, mu (Turkiyya) za mu ci gaba da tunkarar Isra'ila kan rashin imanin da take yi a Gaza, kuma tabbas za ta ɗanɗana kuɗarta kan laifukan da ta aikata," kamar yadda daraktan sadarwa na ƙasar ya ambato Shugaba Erdogan yana f Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi magana ta wayar tarho da takwaransa na Falasɗinu Mahmoud Abbas, inda ya tabbatar masa cewa Isra'ila za ta ɗanɗana kuɗarta kan rashin imanin da take yi ga Falasɗinawan da ke Gaza, a cewar daraktan sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun. Shugaban ya bayyana ƙarara cewa "ko mene ne zai faru, mu (Turkiyya) za mu ci gaba da tunkarar Isra'ila kan hare-haren rashin imanin da take aikatawa a Gaza, kuma tabbas Isra'ila za ta ɗanɗana kudarta sakamakon wannan ɓarnar da take yi," in ji Altun a hira da TRT Haber ranar Juma'a. Daraktan na sadarwa yana bayani ne a wani shiri da aka yi kai-tsaye bayan harin da Isra'ila ta kai wa wata tawagar ƴan jarida da ke aiko da labarai daga sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, wanda ya yi sanadin jikkata ƴan jarida da dama ciki har da ma'aikatan TRT Arabi . An yanke ƙafar mai ɗaukar hotuna da bidiyo na TRT Sami Shehadeh sakamakon raunukan da ya samu. A cewar ganau, da gangan Isra'ila ta kai hari kan tawagar yan jaridar. Shugaba Erdogan ya ce Isra'ila ƙasar "ƴan ta'adda" ce, yana mai cewa tana rayuwa ne bisa dogaro da ci gaba da ta'addanci da kisan kiyashi, kamar yadda Altun ya ambato shi yana cewa. Turkiyya ta yi tir da harin da Isra'ila ta kai wa ƴan jarida da gangan Turkiyya tana goyon bayan Falasɗinu Yayin da yake tattaunawa da Abbas, Erdogan ya jaddada cewa “za a ɗauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da tsagaita wuta Gaza, cikin har da (aiwatar da) ƙudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya,” in ji Altun. Kazalika Erdogan ya yi kira ga ƙasashe su ada kai domin tunkarar Isra'ila, yana mai ƙara yin kira ga Falasɗinawa da ke da rarrabuwar kawuna su haɗa kansu. Altun ya ce tun shekarar 1948 Isra'ila take gallaza wa mutanen yankin, yana mai cewa mahukuntan birnin Tel Aviv sun yi watsi da dukkan gargaɗin da ake yi musu tun da suka ƙaddamar da hare-hare na ranar 7 ga watan Oktoba. "Waɗanda suka yi gum da bakunansu a kan wannan lamari a yanzu, tarihi ba zai taɓa mantawa da su ba," in ji shi, inda ya jaddada cewa Turkiyya, wadda Shugaba Erdogan yake jagoranta, ta tsaya tsayin daka don kare hakkin Falasɗinawa. "Ba don goyon bayan da Turkiyya take yi wa Falasɗinawa ba tun shekarar 2002, da wulaƙancin da za a yi musu ya fi haka muni," in ji Altun. Daraktan sadarwar ya ce Turkiyya ba za ta gajiya ba wajen fallasa dukkan ta'asar da Isra'ila take yi don duniya ta gani ta kafofin watsa labaran TRT, da kamfanin dillancin labarai na Anadolu da dukkan sauran kafafen watsa labarai. "Mu ne murya ta adalci ga Falasɗinu a dukkan ɓangarorin duniya, kuma za mu ci gaba da hakan," in ji shi.