Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 421 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,363 da jikkata fiye da mutum 105,070. A Lebanon kuwa, Isra'ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktoban bara. Aƙalla Falasɗinawa 25 Isra’ila ta kashe a Gaza daga ciki har da ma’aikata uku na ƙungiyar samar da abinci ta World Central Kitchen da kuma jikkata gommai a daidai lokacin da Isra’ila ke ƙara zafafa hare-hare a Zirin Gaza. Majiyoyin kiwon lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa Falasɗinawa bakwai daga ciki har da ma’aikatan World Central Kitchen Isra’ilar ta kashe a wani hari ta sama wanda aka kai kan wata mota da ke ɗauke da farar hula a Khan Younis. A cikin birnin na Gaza kuwa, mutum bakwai Isra’ilar ta kashe a wani hari da ta kai wani gida da ke unguwar Al-Rimal, kamar yadda hukumar kare fararen hula ta Falasɗinawa ta tabbatar. An kashe wasu ƙarin Falasdinawa 10 a wani harin da Isra'ila ta kai kan wani gida a unguwar Shujaiya da ke gabashin birnin Gaza, kamar yadda wata majiyar lafiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu. 0500 GMT — Wakilan Hamas sun nufi birnin Alkahira na Masar domin tattaunawa kan yiwuwar tsagaita wuta a Gaza, kamar yadda wani jami'i na ƙungiyar ta Hamas ya bayyana. Sai dai duka wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta tayar da bam a unguwar Sheikh Radwan da ke cikin birnin Gaza inda ta kashe Falasɗinawa 10. Wani jirgin yaƙin Isra'ila ya kai hari kan wani gida mallakar iyalan as-Sardi da ke unguwar inda farar hula 10 suka rasu, wasu kuma suka jikkata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Isra'ila WAFA ya tabbatar. 0030 GMT — An gudanar da zanga-zanga 105 a biranen Morocco 48 domin nuna goyon baya ga Gaza An gudanar da zanga-zanga 105 a ranar Juma'a a biranen Moroko 48 don yin tir da hare-haren Isra'ila da nuna goyon baya ga Gaza. Dubban jama'a ne suka taru a wuraren da jama'a ke yin zanga-zangar domin amsa kiraye-kirayen kungiyoyin fararen hula, ciki har da hukumar kare muradun al'ummar kasar Morocco. Masu zanga-zangar sun nuna bacin rai da nuna goyon baya ga al'ummar Falasdinu
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 25, ciki har da ma'aikata uku na ƙungiyar World Central Kitchen
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 421 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,363 da jikkata fiye da mutum 105,070. A Lebanon kuwa, Isra'ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktoban bara. Aƙalla Falasɗinawa 25 Isra’ila ta kashe a Gaza...

لمحة سريعة
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 421 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,363 da jikkata fiye da mutum 105,070. A Lebanon kuwa, Isra'ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktoban bara. Aƙalla Falasɗinawa 25 Isra’ila ta kashe a Gaza...
