Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Isra'ila ta kashe ƙarin mutum 47 a sabbin hare-hare a Gaza

A rana ta 331 da Isra’ila ta kwashe tana yaƙi a Gaza, ta kashe Falasɗinawa aƙalla 40,738 – galibinsu mata da yara – tare da jikkata fiye da 94,154 inda hasashe ya bayyana sama da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka yi wa ruwan bam. 1018 GMT — Aƙalla Falasɗinawa 47 Isra’ila ta sake...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:12
Isra'ila ta kashe ƙarin mutum 47 a sabbin hare-hare a Gaza
En bref

A rana ta 331 da Isra’ila ta kwashe tana yaƙi a Gaza, ta kashe Falasɗinawa aƙalla 40,738 – galibinsu mata da yara – tare da jikkata fiye da 94,154 inda hasashe ya bayyana sama da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka yi wa ruwan bam. 1018 GMT — Aƙalla Falasɗinawa 47 Isra’ila ta sake...

A rana ta 331 da Isra’ila ta kwashe tana yaƙi a Gaza, ta kashe Falasɗinawa aƙalla 40,738 – galibinsu mata da yara – tare da jikkata fiye da 94,154 inda hasashe ya bayyana sama da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka yi wa ruwan bam. 1018 GMT — Aƙalla Falasɗinawa 47 Isra’ila ta sake kashewa a Gaza, kamar yadda hukumomi suka tabbatar. Zuwa yanzu adadin mutanen da Isra’ilar ta kashe a Gaza sun kai 40,738 sannan 94,154 suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa tun daga 7 ga watan Oktoba. 0731 GMT — An soma gudanar da rigakafin cutar polio a hukumance a Gaza a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a Gaza. An sanar da soma wannan aikin rigakafin ne bayan da aka samu ɓullar cutar ta polio a karon farko a Gaza bayan shekara 25. Jarirai sabbin haihuwa har zuwa shekara goma da haihuwa an kai su wuraren gudanar da rigakafin domin ba su, inda a daidai lokacin jirage marasa matuƙa suka rinƙa wucewa ta sama, in ji Yasser Shaabane, wanda darakta ne na kiwon lafiya a asibitin al-Awda da ke tsakiyar Gaza. "Akwai jirage marasa matuƙa da dama da ke yawo a tsakiyar Gaza kuma muna fata za a gudanar da wannan rigakafin ga yara lafiya," in ji Shaabane. 0656 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai wasu jerin samame a Hebron, lamarin da ya yi sanadin tsare Falasdinawa 6 da suka hada da mata uku. A cewar kamfanin dillancin labarai na WAFA, an gudanar da samamen ne na musamman a birnin Hebron da garuruwan Halhul da ke arewa da kuma Yatta a kudu. Majiyar ta ruwaito cewa sojojin na Isra'ila sun kai samame a garin Yatta tare da tsare wasu mazauna garin biyu ciki har da Yamama Ibrahim Hirini, wata daliba 'yar shekara 18 a Jami’ar Palestine Polytechnic University.