Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Isra'ila ta dauki matakin dakile ayyukan Hukumar Ƴan Gudun Hijirar Falasdinu ta MDD a Birnin Kudus

Tsawon kwanaki 130, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 28,473 da raunata mutum 68,146. 1357 GMT — Isra'ila ta dauki matakin dakile ayyukan Hukumar Ƴan Gudun Hijirar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:12
Isra'ila ta dauki matakin dakile ayyukan Hukumar Ƴan Gudun Hijirar Falasdinu ta MDD a Birnin Kudus
At a glance

Tsawon kwanaki 130, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 28,473 da raunata mutum 68,146. 1357 GMT — Isra'ila ta dauki matakin dakile ayyukan Hukumar Ƴan Gudun Hijirar...

Tsawon kwanaki 130, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 28,473 da raunata mutum 68,146. 1357 GMT — Isra'ila ta dauki matakin dakile ayyukan Hukumar Ƴan Gudun Hijirar Falasdinu ta MDD a Birnin Kudus da ta mamaye Isra'ila ta kaddamar da matakan dakatar da Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) daga ayyukanta a Gabashin Birnin Kudus, kamar yadda kafafen yada labaran Isra'ila suka bayyana. Shafin watsa labarai na Times of Israel ya rawaito cewa, ministan gidaje na Isra’ila Yitzhak Goldknopf a ranar Litinin ya rubuta wasika zuwa ga daraktan hukumar kula da filaye ta Isra’ila kan korar UNRWA daga duk wani abin da ake kira wata kasa a Birnin Kudus. Ya ba da umarnin “dakatar da” duk wata yarjejeniya tsakanin hukumar da hukumar kula da filaye. 1251 GMT — Isra'ila ta ji wa wakilan Al Jazeera biyu 'mummunan rauni' Kafar watsa labarai ta Al Jazeera a ranar Talata ta ce an raunata ƴan jaridarta biyu a wani hari da Isra’ila ta kai a birnin Rafah da ke kudancin Gaza. Kafar watsa labaran ta ƙasar Qatar ta ce rayuwar wakilinta Abu Omar na cikin hatsari sakamakon an yanke ƙafarsa ta dama. Haka kuma akwai wani wakilinta mai ɗaukar hoto Ahmad Matar wanda ya samu rauni mai yawa tare da zubar da jini. A ƴan kwanakin nan Isra’ila na zafafa hare-hare a birnin Rafah wadda ke kan iyaka da ƙasar Masar.