Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 353, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,431 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,818 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. 1652 GMT — Gwamnatin Isra'ila ta ayyana "yanayi na musamman" dokar ta-ɓaci a duka faɗin ƙasar, har zuwa 30 ga watan Satumba. 1431 GMT — Akalla mutane 274 da suka hada da yara 21 da mata 31 ne suka mutu yayin da wasu 1,024 suka jikkata a hare-haren da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon, in ji ministan lafiya na kasar yayin wani taron manema labarai. 1158 GMT — Isra'ila na shirin kai manyan hare-hare a Beqaa na Lebanon - Sojoji Jiragen saman Isra'ila na shirin kai hari kan katafaren wajen da ake ajiye da manyan makamai na kungiyar Hizbullah a yankin Beqaa na kasar Lebanon, in ji kakakin rundunar sojin Isra'ila, inda ya yi kira ga fararen hula da su gaggauta ficewa. "Abin da ake gani a kudancin kasar Lebanon, shi ne fashewa ta biyu na makaman Hizbullah, wadanda ke tashi a cikin gidaje. A duk gidan da muke kai hari akwai makamai. Roka, makamai masu linzami, jiragen sama marasa matuka wadanda aka yi d nufin kashe fararen hula na Isra'ila," Rear Admiral Daniel Hagari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin. 0700 GMT — Isra'ila ta kashe yara biyar da mata biyu a wani sabon harin da ta kai Gaza Aƙalla Falasɗinawa takwas waɗanda suka haɗa da mata biyu da yara biyar Isra'la ta kashe a wani sabon hari ta sama da ta kai wata makaranta ɗauke da farar hula a tsakiyar Gaza. An kashe wata uwa da 'ya'yanta huɗu haka kuma an jikkata wasu a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai gidan iyalin Al-Samak da ke birnin Deir al Balah, kamar yadda hukumar kare farar hula ta Gaza ta tabbatar. A wata sanarwa ta daban, hukumar kare farar hulan ta kara da cewa harin da Isra'ila ta kai kan makarantar Khaled Bin Al-Waleed da ke sansanin 'yan gudun hijira na Al-Nuseirat, ya kashe wani mutum, matarsa, da 'yarsu, tare da jikkata wasu. 0630 GMT — Gomman hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama a kudanci da gabashin Lebanon sun yi sanadin mutuwar aƙalla farar hula ɗaya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NNA ya tabbatar. “Jiragen yaƙin maƙiya sun ƙaddamar da hare-hare....sama da hare-hare 80 a cikin minti 30”, inda suka afka gundumar Nabatiyeh da ke kudancin Lebanon,” in ji kamfanin dillancin labaran na Lebanon. Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare tsakanin mayaƙan Hezbollah na Lebanon da kuma sojojin Isra’ila.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Isra'ila ta ayyana dokar ta-ɓaci a duka faɗin ƙasar har zuwa 30 ga Satumba
Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 353, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,431 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,818 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. 1652 GMT — Gwamnatin Isra'ila ta ayyana "yanayi na musamman"...

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 353, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,431 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,818 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. 1652 GMT — Gwamnatin Isra'ila ta ayyana "yanayi na musamman"...
