Isra'ila ta aikata laifukan yaƙi a Gaza, ciki har da laifin "karar da al'umma", in ji rahoton Majalisar Dinkin Duniya mai zaman kansa. Mahukuntan Isra'ila na da alhakin "Laifukan yaki kan bil'adama" da suka aikata a lokacin yaƙin Gaza da aka fara tun 7 ga Oktoban 2023, in ji wani sabon rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar. Kwamitin Bincike na Kasa da Kasa na Majalisar Dinkin Duniya ya gano cewar mahukuntan Isra'ila na da alhakin "laifukan yaki na yunwatarwa a matsayin makami da kisan jama'a da gangan da raba mutane da matsugunansu ta karfi da fyade da cutarwa da muzantawa mai tsanani da tsare jama'a ba gaira babu dalili da keta mutuncin dan'adam." Kwamitin ya gano cewa an aikata laifukan yaki da suka hada da "cin zarafin bil'adama da kashe rayuka da dama da zaluntar maza manya da yara kanana Falasdinawa da kisan kai da raba mutane da matsugunansu da cutarwar keta haddi" a Gaza. Kisa da jikkata fararen hula a Gaza da rushe gine-ginen fararen hula a Gaza, sun faru ne saboda shirin aikata hakan da nufin cutarwa mafi muni, an yi watsi da ka'idojin rabe aya da tsakuwa da bambancewa da daukar matakan kula." Rahoton ya kara da cewa "Amfani da munanan makamai manya da ke iya yin barna a yankuna da gangan ya zama "harin ganganci kuma na kai tsaye a kan fararen hula." Game da kalaman da mahukuntan Isra'ila suka yi, rahoton ya ce kalaman nasu "sun zama na zuga da tayar da rikici kuma na iya zama wasu laifuka na kasa da kasa," yana mai karawa da cewar ingiza kisan kiyashi babban laifi ne a karkashin dokokin kasa da kasa. Kwamitin ya kuma auna umarnin kwashe mutane da Isra'ila ta bayar da cewa "ba su isa ba, kuma umarnin na da matsala da rikitarwa, sannan ba su bayar da isasshen lokaci ga jama'a na su bar yankunan ba." "Dadin dadawa, hanyoyin fitar jama'a da kwashe su da aka ce suna da tsaro, sun fuskanci hare-haren sojojin Isra'ila," in ji kwamitin. "Dukkan wannan, ya zama tirsasawa su bar gidajensu." Isra'ila ta kuma 'mamayi' Gaza wadda "ukuba ce ga al'umma baki daya" wanda ya keta haddin fararen hula, in ji rahoton na MDD. "Mahukuntan Isra'ila sun aike da makamai ga mayakansu a yankunan da suka yi wa kawanya, kuma run yi amfani da kayan da ke kubutar da rayuwa kamar ruwan sha da abinci da lantarki da man fetur da taimakon jinkai, a matsayin dabarun yaki da karfin ikon siyasa." Kwamitin ya kuma jaddada cewar mamayar ta "yi tasiri kan kowa" ciki har da mata masu juna biyu da nakasassu, da kuma raunata yara kanana da suke kamuwa da cututtukan da ke da alaka da yunwar da rashin abinci ta jawo." Game da abubuwan da ake yi a Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye, kwamitin ya gano cewa Isra'ila ta aikata "fyade da cutarwa da muzanta wa dan'adam da ukuba marar dadi, wadanda dukkan su laifukan yaki ne." Haka kuma, kwamitin na MDD ya kaddara cewar gwamnatin Isra'ila tare da rundunar sojin kasar, "sun bayar da izini da bayar da dama da taimakawa ingiza" yakar falasdinawa a Yammacin gabar Kogin Jordan. Binciken Majalisar Dinkin Duniya kan Isra'ila da Hamas A shawarwarin da ya bayar, kwamitin ya bukaci Isra'ila da ta gaggauta daukar mataki, ciki har da na tsagaita wuta da kawo karshen mamayar Gaza da tabbatar da an kai kayan agaji da kawo karshen hare-hare kan fararen hula da dukiyoyinsu. Hukumar ta kuma yi kira ga Tel Aviv da ta yi "Cikakken aiki da" doka da oda da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ta fitar a 26 ga Janairu da 28 ga Maris da 24 ga Mayu, kuma musamman ma umarnin bai wa kwamitin damar shiga Gaza don gudanar da bincike. Ya kuma bayar da shawarar cewa dukkan kasashen da suka sanya hannu kan Yarjejeniyar Rome, ya kamata su yi aiki da Matakan Kotun Hukunta Manyan laifuka ta Kasa da Kasa. "Dole ne Isra'ila ta dakatar da ayyukan soji da hare-hare Gaza, ciki har da hare-hare kan Rafah, wanda ya janyo mutuwar daruruwan fararen hula, tare da raba dubbai da matsugunansu inda suka tafi yankunan da ba su da tsaro," in ji shugaban kwamitin Navi Pillay, a wata sanarwar manema labarai da ya fitar. Game da harin 7 ga Oktoba da aka kai Isra'ila, kwamitin ya samu bangaren soji na kungiyar Hamas da wasu kungiyoyin Falasdinawa shida da ke daukar makamai, da alhakin "aikata laifukan yaki da gangan, kai hare-hare kan fararen hula, kisa da cutarwa, tare da muzanta dan adam ta hanyar ukuba mai tsanani, rusawa ko ƙwace kadarorin makiyi da cin fuska, da kama fursunonin yaki, da suka hada da yara kanana." Kwamitin ya kuma bukaci gwamnatin Kasar Falasdinu da shugabannin da suke Gaza da su "gaggauta dakatar da hare-haren makaman roka zuwa Isra'ila, su saki fursunoni ba tare da wasu sharudda ba, sannan su gudanar da bincike tare da hukunta wadanda ke da hannu a wannan dnayen aiki, ciki har da wadanda suka kai harin 7 ga Oktoban 2023." A ranar 19 ga Yuni za a mika rahoton kwamitin ga Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam ta MDD a yayin zaman ta na 56 a Geneva. Kwamitin ya ce ya tattara bayanansa ne bayan tattaunawa da wadanda yakin ya shafa da kuma tuntubar shaidu na kusa da na nesa, da samun bayanai a yayin zuwa Turkiyya da Masar, tare da samun dubban majiyoyi da aka tabbatar da ingancinsu ta hanyar nazarin kwakwaf da daruruwan bayanai da aka miƙo da hotunan da tauraron dan'adam ya dauka da nazarin kwakwaf na jami'an lafiya. "Isra'ila ta kawo cikas ga binciken kwamitin tare da hana shi shiga Isra'ila da yankunan Falasdinawa da ta mamaye," in ji rahoton.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Isra'ila ta aikata laifukan yaƙi a Gaza: Rahoton MDD
Isra'ila ta aikata laifukan yaƙi a Gaza, ciki har da laifin "karar da al'umma", in ji rahoton Majalisar Dinkin Duniya mai zaman kansa. Mahukuntan Isra'ila na da alhakin "Laifukan yaki kan bil'adama" da suka aikata a lokacin yaƙin Gaza da aka fara tun 7 ga Oktoban 2023, in ji wani sabon rahoto da...

Isra'ila ta aikata laifukan yaƙi a Gaza, ciki har da laifin "karar da al'umma", in ji rahoton Majalisar Dinkin Duniya mai zaman kansa. Mahukuntan Isra'ila na da alhakin "Laifukan yaki kan bil'adama" da suka aikata a lokacin yaƙin Gaza da aka fara tun 7 ga Oktoban 2023, in ji wani sabon rahoto da...
