"Isra'ila na ƙoƙarin kawar da wanzuwar mutane gaba ɗaya da su da al'adunsu. Hare-haren da Isra'ila ta kai a yankin Rafah, inda ta kori mutane a 'yan kwanakin nan, babban misali ne na manufofinta na kisan kare dangi," Altun ya faɗa. Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya jaddada cewa, ba za a iya yin biris ga farfagandar watsa labaran ƙarya da Isra'ila ke yaɗawa ba, domin irin wannan halin ko in kula na iya haifar da a dinga ganin kamar laifukan da ƙasar ke aikatawa daidai ne. Da yake jawabi a wani taron da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya shirya a ranar Talata, Altun ya bayyana cewa, “Tare da irin wadannan abubuwan, da ayyukan da muke yi a fagen, da kuma hotunan da muke tattarawa, za mu rubuta bayanai kan kisan kiyashin da Isra’ila ta yi ba a matsayin ‘zargi’ ba amma a matsayin ‘tabbatacciyar shaida, da tabbatattun laifukan yaƙi.' Yunƙurinmu yana kan wannan al'amari." "A yau Isra'ila na aikata wani babban laifi na kisan ƙare dangi a Gaza. Isra'ila ta aikata kuma tana ci gaba da aikata manyan laifuka da dama da aka sanya su a karkashin yarjejeniyar Rum, musamman kisan kiyashi." "Kisan ƙare dangi ba wai aikin kashe jama'a ba ne kawai. Kisan ƙare dangi wani babban hari ne akan zahiri da ruhin mutane. Isra'ila ba kawai tana kashe mutanen da ke zaune a Gaza a lokaci guda ba ne, har ma da yin kisan ƙare dangi na al'adu don lalata rayuwar kafatanin yankin," in ji shi. "Isra'ila na ƙoƙarin kawar da wanzuwar mutane gaba ɗaya da su da al'adunsu. Hare-haren da Isra'ila ta kai a yankin Rafah, inda ta kori mutane a 'yan kwanakin nan, babban misali ne na manufofinta na kisan kare dangi," Altun ya faɗa. Babban jami'in ya kuma ja hankali kan muhimmancin littafin da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya wallafa mai ɗauke da hotunan da ke tabbatar da laifukan da Isra'ila ke aikatawa a Gaza, wanda aka gabatar da shi ga kotun ƙasa da ƙasa (ICJ).
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Isra'ila ta aikata gagarumin laifin kisan ƙare dangi a Gaza: Altun
"Isra'ila na ƙoƙarin kawar da wanzuwar mutane gaba ɗaya da su da al'adunsu. Hare-haren da Isra'ila ta kai a yankin Rafah, inda ta kori mutane a 'yan kwanakin nan, babban misali ne na manufofinta na kisan kare dangi," Altun ya faɗa. Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya jaddada cewa, ba...

"Isra'ila na ƙoƙarin kawar da wanzuwar mutane gaba ɗaya da su da al'adunsu. Hare-haren da Isra'ila ta kai a yankin Rafah, inda ta kori mutane a 'yan kwanakin nan, babban misali ne na manufofinta na kisan kare dangi," Altun ya faɗa. Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya jaddada cewa, ba...
