Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Isra’ila na shan suka kan kisan ma’aikatan agaji a Gaza

Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 179 - ya kashe Falasdinawa akalla 32,916 tare da raunata wasu 75,494 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki. 1411 GMT — Isra'ila ta kashe sama da ɗalibai 6...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:12
Isra’ila na shan suka kan kisan ma’aikatan agaji a Gaza
A taƙaice

Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 179 - ya kashe Falasdinawa akalla 32,916 tare da raunata wasu 75,494 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki. 1411 GMT — Isra'ila ta kashe sama da ɗalibai 6...

Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 179 - ya kashe Falasdinawa akalla 32,916 tare da raunata wasu 75,494 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki. 1411 GMT — Isra'ila ta kashe sama da ɗalibai 6,000 da malamai 266 a Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan Sama da ɗalibai 6,000 Isra’ila ta kashe tun bayan da ta soma kai hare-hare a Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan a ranar 7 ga watan Oktoba. A wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta Falasɗinu ta fitar, ta ce sama da ɗalibai 5,994 aka kashe da raunata 9,890 a Gaza. Sannan an kashe ɗalibai 56 da raunata 329 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan. Sanarwar ta ce an kashe malaman makaranta 266 da raunata 973 a Gaza tun bayan soma yaƙin. 1526 GMT — Isra’ila na shan suka kan kisan ma’aikatan agaji a Gaza Ƙasashe da dama da ƙungiyoyi masu zaman kansu a faɗin duniya na caccakar Isra’ila kan kashe ma’aikatan agaj na ƙungiyar World Central Kitchen a Gaza. Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ransa ya ɓaci matuƙa kan kisan ma’aikatan. Ƙasar Canada a nata ɓangaren, ta yi Allah wadai da kisan sojojin inda ta buƙaci a gudanar da bincike. Ita ma ƙasar Jamus a ranar Talata ta buƙaci Isra’ila ta gudanar da bincike mai zurfi kan kisan ma’aikatan. 1453 GMT — Netanyahu ya tabbatar da batun kashe ma'aikatan agaji a Gaza Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da cewa sojojin Isra’ila sun kashe ma’aikatan agaji a Gaza. A ranar Litinin ne sojojin na Isra’ila suka kai hari kan ma’aikatan agajin World Central Kitchen na Amurka inda suka kashe bakwai. Netanyahu ya ce “dagangan aka kashe ma’aikatan ba” kuma za a gudanar da bincike,” kamar yadda jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila ta ruwaito.