Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Isra'ila gwamnati ce mai ɓarna da ke ciyar da kanta da rikici maimakon tsarin doka - Duran

Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta karbi baƙuncin wani taro da aka yi wa take da "Gaza: Humanity's Litmus Test". Daraktan Sadarwa na Turkiyya Burhanettin Duran ya ce "duniya na fama da matsalar Isra'ila", yana mai bayyana ta a matsayin gwamnati mai ɓarna da ke keta dokokin ƙasa da ƙasa da kuma ciyar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:12
Isra'ila gwamnati ce mai ɓarna da ke ciyar da kanta da rikici maimakon tsarin doka - Duran
At a glance

Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta karbi baƙuncin wani taro da aka yi wa take da "Gaza: Humanity's Litmus Test". Daraktan Sadarwa na Turkiyya Burhanettin Duran ya ce "duniya na fama da matsalar Isra'ila", yana mai bayyana ta a matsayin gwamnati mai ɓarna da ke keta dokokin ƙasa da ƙasa da kuma ciyar...

Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta karbi baƙuncin wani taro da aka yi wa take da "Gaza: Humanity's Litmus Test". Daraktan Sadarwa na Turkiyya Burhanettin Duran ya ce "duniya na fama da matsalar Isra'ila", yana mai bayyana ta a matsayin gwamnati mai ɓarna da ke keta dokokin ƙasa da ƙasa da kuma ciyar da kanta da rikici maimakon tsarin doka.’’ Kalaman Duran sun zo ne a ranar Laraba yayin taron "Gaza: Humanity’s Litmus Test", wanda aka gudanar a Hukumar Sadarwar Turkiyya da ke Ankara inda jami'an diflomasiyya, da malamai da kuma 'yan jarida suka gabatar da jawabai. A jawabin da ya gabatar na musamman, Duran ya jaddada matsayin Turkiyya ƙarkashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan na: tabbatar da samar da hanyoyin tsagaita wuta na dindindin, tare da tabbatar cewa an isar da kayayyakin jinƙai, da kuma kafa ƙasar Falasdinu mai cin gashin kanta tare da Gabashin Kudus a matsayin babban birninta. Ya jaddada cewa "al'ummar duniya ba za su iya yin watsi da gaskiyar abin da Isra'ila ke yi ba, wanda ke barazana ga zaman lafiyar yanki da ma duniya baki daya." Sanya batun Gaza a kan gaba a duniya Duran ya jaddada rawar da hukumar sadarwa ta Turkiya ke takawa wajen tallafa wa Falasɗinu a "ɓangaren sadarwa." Ta hanyar amfani dabarun diflomasiyya da kayan aikin yada labarai na zamani, a cewar Daraktan "gaskiyar yanayin da Gaza ke ciki zai kasance a kan a ajandar duniya." Ya yi ƙarin haske game da koƙarin da aka yi wajen fallasa sama da ƙarairayi 250 na Isra'ila, wanda ya kai ga sadaukarwar mujalloli da manyan tarukan ƙasa da ƙasa, da na baje-koli da kuma tura ‘yan jarida wurare don ɗaukar sahihan labarai. "Sadarwa a gare mu ba kawai hanyoyin samun ilimi ba ne, batu ne na lamiri," in ji Duran. "Muna ƙoƙarin fakar da duniya tare da tabbatar da cewa an adana tarihin munanan ayyukan da Isra'ila ta aikata." Kafofin sadarwa a kan gaba